• Leadership Hausa
Thursday, March 23, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zabtare Dala Miliyan 418 A Bashin Paris Club: Gwamnoni Sun Mayar Wa Malami Martani

by Abubakar Abba
7 months ago
in Kananan Labarai
0
Zabtare Dala Miliyan 418 A Bashin Paris Club: Gwamnoni Sun Mayar Wa Malami Martani
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kungiyar Gwamnonin kasar nan sun nuna damuwarsu a kan furucin Miinistan Shari’a kuma Atoni-Janar na kasa Abubakar MalamI kan maganar biyan bashin dala miliyan 418 da ake bin wasu ‘yan Kwangila da wasu masu aikin tuntuba na kudin Paris Club.

Kungiyar ta kuma yi mamakin kan yadda Malami ya dage wajen tura kudaden na Paris Club ga wasu daidaikun jama’a masu zaman kansu alhali gwamnonin sun karyata ikirarin na masu aikin tuntuba wanda a yanzu, maganar na a gaban kotu.

  • Obasanjo Ya Roki Marayun Borno Su Yafe Wa ‘Yan Ta’addar Da Suka Kashe Iyayensu
  • Akwai Alamun Ba Gudu Ba Ja Da Baya A Kan Batun Taiwan

Mai magana da yawun kungiyar Abdulrazaque Bello-Barkindo ne, ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabin na Channels.

Barkindo ya sanar da cewa, kamata ya yi a bar kotun ta yanke hukunci kan maganar wacce ta ke a gabanta.

A cewarsa, “Mun dogara ne a kan umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da kuma tsimayi daga gun kotun don ta yanke hukunci a kan batun”.

Labarai Masu Nasaba

NIS Reshen Ribas Ta Kafa Kwamitin Bunkasa Walwalar Jami’ai

Zaben Gwamnoni: Ku Ankare Akwai Masu Shaidar Aikin Tsaro Ta Bogi, INEC Ga Masu Zabe

Barkindo ya kara da cewa, kamata ya yi mutane su tambayi Malami kan mene ne ya sa yake gaggawar biyan kudaden ga wasu daidaikun mutane bayan alhali maganar na a gaban kotu.

Ya ce, “Muna fadar hakan ne domin Ikirarin ba gaskiya bane domin maganar na gaban kotu kuma ita ce, za ta yanke hukuncin”.

Kakakin ya ce, kamata ya yi Malami ya jira kotun ta yanke hukunci kan maganar, inda ya kara da cewa, gwamnonin ba su da wani ja kan biyan kudaden.

In ba a manta ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 3 ga watan Agustan shekarar 2022 ne a taron Majalisar kasa, ya umarci Ministar kudi Zainab Ahmed, da ta dakatar da shirin fara gudanar da zabtare kudaden na Paris Club dala miliyan 418 har idan kotu ta yanke hukunci kan maganar.

Tags: BuhariGwamnoniKotuMalamiParis ClubZainab Idris
ShareTweetSendShare
Previous Post

Obasanjo Ya Roki Marayun Borno Su Yafe Wa ‘Yan Ta’addar Da Suka Kashe Iyayensu

Next Post

Salman Rushdie: Wanda Ya Yi Batanci Ga Annabi Na Cikin Mawuyacin Hali Bayan Kai Masa Hari

Related

NIS
Kananan Labarai

NIS Reshen Ribas Ta Kafa Kwamitin Bunkasa Walwalar Jami’ai

1 day ago
INEC Ta Kara Wa’adin Karbar Katin Zabe
Kananan Labarai

Zaben Gwamnoni: Ku Ankare Akwai Masu Shaidar Aikin Tsaro Ta Bogi, INEC Ga Masu Zabe

5 days ago
Shugabar Matan NNPP Reshen Abuja Ta ‘Yanta Fursunoni 4
Kananan Labarai

Shugabar Matan NNPP Reshen Abuja Ta ‘Yanta Fursunoni 4

1 month ago
Dan’asabe Ya Janye Kalaman Da Ya Yi A Kan Babban Asibitin Wudil
Kananan Labarai

Dan’asabe Ya Janye Kalaman Da Ya Yi A Kan Babban Asibitin Wudil

2 months ago
Gwamnatin Bauchi Ta Fayyace Zare Da Abawa Kan Filin Makabarta A Yolan Bayara
Kananan Labarai

Gwamnatin Bauchi Ta Fayyace Zare Da Abawa Kan Filin Makabarta A Yolan Bayara

2 months ago
Tambuwal Ya Gabatar Da Kasafin Kudinsa Na Karshe a Sakkwato
Kananan Labarai

Tambuwal Ya Gabatar Da Kasafin Kudinsa Na Karshe a Sakkwato

4 months ago
Next Post
Salman Rushdie: Wanda Ya Yi Batanci Ga Annabi Na Cikin Mawuyacin Hali Bayan Kai Masa Hari

Salman Rushdie: Wanda Ya Yi Batanci Ga Annabi Na Cikin Mawuyacin Hali Bayan Kai Masa Hari

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Kammala Ziyararsa A Kasar Rasha Cikin Nasara

Xi Jinping Ya Kammala Ziyararsa A Kasar Rasha Cikin Nasara

March 23, 2023
Matawalle Ya Karbi Faduwa, Ya Yi Fatan Alheri Ga Sabon Gwamnan Zamfara

Matawalle Ya Karbi Faduwa, Ya Yi Fatan Alheri Ga Sabon Gwamnan Zamfara

March 23, 2023
Siyasantar Da Batun Gano Asalin COVID-19 Dabara Ce Ta Boye Gaskiya

Siyasantar Da Batun Gano Asalin COVID-19 Dabara Ce Ta Boye Gaskiya

March 23, 2023
Jirgin Saman Nijeriya Zai Fara Aiki Kafin Ranar 29 Ga Mayu

Jirgin Saman Nijeriya Zai Fara Aiki Kafin Ranar 29 Ga Mayu

March 23, 2023
Ina So A Ko’ina A Ji Hikima Da Fasaharmu – Yusuf King

Ina So A Ko’ina A Ji Hikima Da Fasaharmu – Yusuf King

March 23, 2023
Hadin Gwiwar Sin Da Rasha Na Da Muhimmanci Sosai Ga Duniya

Hadin Gwiwar Sin Da Rasha Na Da Muhimmanci Sosai Ga Duniya

March 23, 2023
Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumin Gobe A Wasu Birane

Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumin Gobe A Wasu Birane

March 23, 2023
Gyare-gyare Su Kan Faru Ne Bisa Sauyawar Tunanin Mutum

Gyare-gyare Su Kan Faru Ne Bisa Sauyawar Tunanin Mutum

March 23, 2023
NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Saboda Karancin Kudi A Nijeriya

NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Saboda Karancin Kudi A Nijeriya

March 23, 2023
FEC Ta Amince Da Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Wajen Gina Barikin Jami’an NDLEA

FEC Ta Amince Da Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Wajen Gina Barikin Jami’an NDLEA

March 23, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.