A wannan makon zan mayar da hankali ne a kan dabi’a, musamman ma batun da ya shafi gini da rusa dabi’ar mutum, shin za a iya ko a’a? idan za a iya, ta wadanne hanyoyi ne za ka iya sauya dabi’ar mutum daga wani aiki zuwa ga wani?
Kafin ka iya sauya dabi’ar mutum ka na bukatar ka auna yanayin fahimtarsa da kuma yadda ya ke tunani.
- Taron Sin Da Afrika A Alkahira Ya Bayyana Muhimmancin Kyautata Dangantakar Bangarorin Biyu
- CICPE Karo Na 5 Zai Mayar Da Hankali Kan Kirkire-Kirkiren Fasahohin Zamani
Misali a nan shi ne, ta ya za a ka iya gamsar da mutum a kan ya fara motsa jiki, alhali a ko da yaushe ya kan yi korafi dangane da rashin lokaci, ko kuma ya cika son jikinshi, ma’ana ba ya son wahala? A irin wannan yanayin, mafita daya ce za ka yi amfani da ita wurin sauya dabi’ar mutum, shi ne ka bijiro mishi da wani sabon bayani wanda bai san da shi ba.
Misali, wanda ka ke son ya fara motsa jiki amma ya ke ce ma ba shi da lokaci, sai ka fara yi mishi bayanin yadda ka ke samarwa kanka da lokaci a kowacce rana har ka ke iya samun daman motsa jiki, kuma a sanadiyyan motsa jikin har ma ka je likitoci sun gwada ka sun tabbatar da cewa a tsawon watanni ka kara lafiya da kuzari, har ma ka samu waraka daga ciwon Basir din da ke addabanka. Wannan bayanin da za ka yi mishi zai sa kwakwalwarshi ta fahimci wani abu, sannan tunaninshi dangane da motsa jiki zai sauya.
Rusa dabi’ar mutum na bukatar a sa kokari da jajirjircewa, saboda abu ne da ke daukar lokaci. Sai dai matukar a ka bi matakan da suka dace, a na iya nasara. ba a son mutum ya kwallafa rai a kan cewa zai iya rusa dabi’ar wani a dan kankanin lokaci.
Kamar yadda ba a lokaci guda a ke gina dabi’u ba, haka nan ba zai yiwu a rusa su a lokaci guda ba. mutum na gina dabi’a ne ta hanyar yin mu’amala da mutane. Gina dabi’un na farawa daga shekarun yarinta, saboda a sannan ne a ke koyon al’adu, tarbiyya da girmama manya. Har zuwa mutuwan mutum ya na mu’amala ne da mutane ya na gina sabbin dabi’u.
Iyaye su ne ke ginawa yara dabi’un farko, shi ne ma ya sa a ke so su rika kiyaye irin maganganun da za su rika yi a gaban yaransu, sannan su tsaftace mu’amalolinsu ta yadda yaran ba za su rika kwaikwayon abubuwan da ba su dace ba. hatta da yin dakuwa da nufin zagi, a wurin iyaye yara ke fara koyo. Shi ne ya sa za ka ga wani ya zama gwani a zagi, kwararren gaske. Ba a sama ya samo dabi’ar ba, abin da ya taso ya ga a na yi a gidansu kenan. Wasu kuwa gidansu mutanen kirki ne, don haka ba su iya samun daman kwaikwayon zagi a gida.
Daga gida, lokacin da yaro ya fara wayo, ma’ana zai yiwu a kyale shi ya rika fita waje, sannan ya kai shekarun fara zuwa makaranta. Wasu unguwarsu ‘G.R.A’ ne, babu hayaniya; ba irin unguwannin nan ba ne da a ke cakude da juna. A nan, dabi’un yaransu sun fi samuwa a mu’amalar da yaran ke kwaikwayo daga iyaye.
A irin unguwannin da a ke cakude, ma’ana wadanda yawanci ma gidajen haya ne masu mutane rututu, ya na wahala a iya saita dabi’un yaro. Na farko yaro zai rika kwaikwayon dabi’un iyayenshi, sannan zai rika kwaikwayon na ‘yan hayan gidansu, sannan zai rika kwaikwayon na sauran yaran kan layi; da ya ke irin wannan unguwannin kofofi a bude su ke, yaro ko da rarrafe ya ke yi, zai iya fita kan layi. Wasu yaran ma, dabi’un da su ke kwaikwayo wa a kan layi, ya fi karfin sanin iyayensu. A irin wadannan unguwannin mutane sun fi saurin diban dabi’u, masu kyau da marasa kyau.
Idan yaran wadanchan unguwannin ‘G.R.A’, suka fara zuwa makaranta, za su iya haduwa da yaran unguwannin da a ke cakude da juna. A makaranta za su fara musayar dabi’u a tsakanin juna. Mutum ya na kwance a gida, ya yi tsammanin dabi’unshi da na matarshi da mutanen cikin gida kadai dansu ke kwaikwaya, bai san cewa ya na kwaikwayo wasu daga mu’amalarshi da wasu yara a makaranta ba. wannan na faruwa hatta a makarantun Islamiyyoyi.
Ba kawai a yarinta a ke gina dabi’u ko kwaikwayonsu ba, kowanne mataki na rayuwa a na sake kwaikwayon dabi’u ne da gina sabbi. Wani zai taso har ya balaga da dabi’u masu ban sha’awa da burgewa, amma da zaran ya fara makarantar Sakandare ko gaba da Sakandare, sai yanayin mu’amalarsa ta chanza, saboda haduwa da zai yi da wasu sabbin mutane wadanda suka fito daga wurare mabambanta. Idan ba a yi sa’a ya hadu da abokan arziki ba, sai ya hadu da wadanda a hankali za su gina mishi dabi’un shaye-shaye, ko kuma neman mata.
Musamman a jami’o’i, wata yarinyar za ta zo daga gidansu da dabi’un kwarai, babu ruwanta da sa suturar banza. Yawancin irin wadannan ‘yan matan, a kan hada su zama dakin ‘Hostel’ daya da su. Tun kafin ta fara halartan azuzuwa don daukan darasi, tun kafin ta san sauran mutanen ajinsu, da wadannan abokan zaman nata za ta fara mu’amala. Idan ba a dace ba, a hankali za su koya mata dabi’ar fita babu lullubi ballantana hijabi. Idan samarinsu sun zo zance, sai su rika takura mata a kan ta yi musu rakiya, har watarana abokin saurayin ya ganta ya ce ya na so, shi kenan ita ma ta shiga shirgin.
Kowacce irin dabi’ar mutum, idan a na son a rusa ta, ba a garaje, ba a gaggawa, ba kuma a nuna kosawa. A hankali za a rika nunawa wannan dabi’ar rashin dacewarta, da kuma nakasunta. Ba a rusa dabi’a da karfi ko da fada, ba a rusa ta da iko ko nuna isa. Dabi’u sun fi bukatar lalama da sassauci.
Kafin ka iya rusa dabi’ar mutum, dole sai ka yi nazarin yadda ya ke kallon wannan dabi’a ta sa, ma’ana fahimtarsa dangane da dabi’ar. Idan Yaro ne wanda ke shaye – shaye, dole ne sai ka fahimci menene fahimtarsa dangane da shaye-shaye, tare da nazarin abubuwan da suka jefa shi zuwa ga shaye – shayen. Shin akwai wani abu da ya ke kauna? Idan akwai menene wannan abin? Shin ya na samun daman yin tunani, wanda ba a maye ba, a hankalinshi? Idan ya kan samu lokacin yin tunani ba tare da ya sha komi ba, sai ka fahimci wannan lokacin, a sannan ne za a iya fara aikin chanza mishi tunani.
Kafin mutum ya fara wannan dabi’a da a ke son rusawa, dole a baya ya na da wasu dabi’u, kuma ya na da wasu abokai wadanda a bayan ya ke mu’amala da su. Dole a na bukatar sannan wannan. Saboda idan dabi’ar ta yi kamari, dole ne sai an sake dawo mishi da rayuwar da ya yi a baya, an dawo mishi da tsofaffin abokai, sannan a shimfida musu tsarin yadda za su tafiyar da mu’amala a tsakaninsu, idan a ka bi matakan yadda suka dace a kan yi nasarar rusa dabi’ar da ba a so. Sai dai hanzari ba gudu ba, kwaikwayon dabi’a ya fi sauri a kan rusa ta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp