Majalisar wakilai ta umurci kwamitinta mai kula da harkokin zabe da ya binciki hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), kan jinkirin gudanar da zaben cike gurbi a majalisun tarayya da na jihohi.
Majalisar ta kuma umarci kwamitin da ya gayyaci shugabannin hukumar ta INEC domin bayyana dalilan da suka janyo tsaikon da kuma matakan da ake dauka na shawo kan lamarin.
- An Bude Cibiyar Tattarawa Da Yada Labarai Ta Taruka Biyu Na Sin
- Gwamnatin Kano Za Ta Ɗau Nauyin Ɗalibai 1,002 Domin Karatu A Ƙasashen Waje
Ana sa ran kwamitin zai bayar da rahoto a cikin makonni hudu don aiwatar matakin majalisa.
Wannan kudiri ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa Jafaru Leko ya gabatar.
A cikin kudirin nasa, Leko ya yi nuni da cewa, tun bayan zaben shekarar 2023, kujeru da dama na ‘yan majalisar dokoki na kasa da na jihohi sun zama babu kowa, sakamakon murabus, ko mutuwa, ko nada tsofaffin ‘yan majalisa kan mukaman zartarwa.
Ya kara da cewa rashin gudunar da daga wurin INEC abu ne mai hadari, wanda ya saba wa dokokin tsarin mulki da dokoki wadanda suka tilas zaben cike gurbi a duk lokacin da aka samu bukatan hakan.
Rahotanni sun bayyana cewa a halin yanzu akwai kujeru bakwai a majalisar kasar nan da babu kowa, akwar biyar a majalisar wakilai, sannan akwai biyu a majalisar dattawa.
Kujerun da babu kowa a majalisar wakilai akwai a jihohin Edo da Oyo da Kaduna da Ogun da kuma Jigawa, yayin da kujerun majalisar dattawan na jihohin Edo da Anambra.
Biyu daga cikin wadannan kujeru sun zama babu kowa ne bayan zaben gwamnan a Jihar Edo, yayin da sauran biyar suka zama babu kowa saboda mutuwar ‘yan majalisa.
Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebolo da mataimakinsa, Denis Idahosa, sun kasance ‘yan majalisar tarayya da ke wakiltar Edo ta tsakiya a majalisar dattawa da kuma mazabar tarayya ta Obia a majalisar.
Sauran kujerun da ba su da kowa sun hada da na marigayi Sanata Ifeanyi Ubah (Anambra South), Isa Dogonyaro (Jigawa), Ekene Abubakar Adams (Kaduna), Olaide Akinremi (Oyo) da Adewunmi Oriyomi Onanuga (Ogun).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp