Kotun majistare da ke zamanta a Sabo, Yaba, Jihar Legas, a ranar Talata, ta wanke fitaccen mawakin nan, Abdulazeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley, dangane da rasuwar Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad.
Gidan Talabijin na Channels TB ya ruwaito cewa Alkalin kotun Majistare Ejiro Kubenje, wanda ya karanta tare da aiwatar da shawarwarin shari’a da hukumar kula da kararrakin jama’a ta Legas ta bayar, ta ce Naira Marley bai da wani laifi da zai amsa.
- CBN Ya Umarci Daraktocin Bankuna Su Mayar Da Bashin Da Suka Karba Ko Su Yi Murabus
- Jama’ar Duniya Sun Soki Matakin Amurka Na Matsawa Kasashe Ta Hanyar Kakaba Haraji
Tare da haka, Naira Marley, kotun ta ce ta saki wani mai tallata waka, Samson Balogun, wanda aka fi sani da Sam Larry; Owodunni Ibrahim, wanda kuma ake kira Primeboy; da tsohon manajan Mohbad, Opere Babatunde.
DPP, duk da haka, ta ce za ta gurfanar da ma’aikaciyar jinya da ta yi wa Mohbad, Feyisayo Ogedengbe, da daya daga cikin abokan Mohbad, Ayobami Sadik shari’a kan laifin rashin kulawa da sakaci da ya saba wa sashi na 251 (e) na dokar laifuka, Ch C.17, Bol.3, Dokokin Jihar Legas, 2015.
Za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotun majistare.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp