Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta gamu da cikas a kokarinta na darewa kan teburin gasar Laliga ta kasar Sifaniya, bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Real Betis a filin wasa na Benito Villamarin da ke Seville.
Tsohon dan wasan Real Madrid, Isco Alacon ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasa a wasan na ranar Asabar. Isco ya na daya daga cikin ‘yan wasan da suka lashe kofin Turai biyar tare da Real Madrid.
- Barcelona Na Cigaba Da Matsawa Real Madrid Lamba
- Mbappe Da Bellingham Ba Za Su Buga Wasan Da Real Madrid Za Ta Kara Da Leganes Ba
Real Madrid ce ta fara jefa kwallo ta hannun Brahim Diaz, kafin Johnny Cardoso ya farke wa masu masaukin bakin ana dab-da tafiya hutun rabin lokaci, Isco ya mayar da wasan danye bayan kwallon da ya jefa a minti na 54 da fara wasan.
Real Madrid wadda ke matsayi na biyu a gasar La Liga, sun buga wasanni 26, inda su ka samu nasara a wasanni 16, aka buga canjaras a wasanni 6, yayin da aka doke ta a wasanni 4.
Isco wanda ya shafe shekaru 9 a Santiago, ya jagoranci ‘yan wasan Betis a matsayin kyaftin a wasan na mako na 26.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp