Gwamnatin Jihar Nasarawa ta samu nasarar jawo kamfanoni 10 da suka zuba jarin dala miliyan 466 a fannoni daban-daban na tattalin arziki a shekarar 2024.
Bugu da ƙari, wasu kamfanoni tara sun yi alkawarin zuba dala miliyan 767, wanda aka rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimta. Rahoton hukumar zuba jari da ci gaban Nasarawa (NASIDA) ya nuna cewa jihar ta samu jimillar jarin dala biliyan 1.2 a 2024.
- Tinubu Zai Halarci Zikirin Juma’a A Fadar Aminu Ado Ta Nassarawa
- Kotu Ta Sake Dakatar Da Sarki Ado Daga Gyara Fadar Nassarawa
Daga cikin manyan kamfanonin da suka zuba jari akwai Juiling Lithium Industry Limited da ke gina masana’antar sarrafa lithium a karamar hukumar Nasarawa da kuɗin dala miliyan 250.
Wasu daga cikin sauran kamfanonin sun haɗa da Future Granary Project ($200m), Husk Power Systems ($7m), da Greenville LNG Compressed Natural Gas ($1.2m).
Har ila yau, Infinitum Energy Group daga Amurka ta shirya saka dala miliyan 180 a fannin samar da wutar lantarki ta hanyoyin amfani da sharar gida da hasken rana.
Ana sa ran waɗannan sabbin jarin za su samar da ayyuka 3,940 a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp