Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mojisola Meranda, ta yi murabus daga mukaminta a ranar Litinin yayin zaman majalisar.Â
Ta ce ta yanke wannan shawara ne domin kare martabar majalisar.
- Kasancewar Zaman Lafiya Na Dogon Lokaci Tsakanin Sin Da Amurka Abu Ne Da Ya Zama Wajibi
- Kwastam Da Hukumar NPA Sun Kulla Hadakar Bunkasa Ingancin Aiki A Tashoshin Jiragen Ruwa
Haka kuma, Mataimakin Kakakin Majalisar, Mojeed Fatai, shi ma ya sauka daga muƙaminsa.
Rahotanni sun nuna cewa Meranda ta ajiye kujerarta ne bayan wata ganawa da tsohon kakakin majalisar, Mudashiru Obasa, wanda ke rikici da shugaban jam’iyyar APC na Legas, Cornelius Ojelabi, da kuma Antoni Janar na jihar, Lawal Pedro.
Bayan murabus ɗinta, an sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakin majalisar, ƙasa da watanni biyu bayan tsige shi.
Haka kuma, an sake zaɓar Mojisola Meranda a matsayin mataimakiyar kakakin majalisar bayan sauka daga matsayinta na kakakin majalisar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp