Kwamitin majalisar dattawa mai kula da da’a, gata, da sauraren kararrakin jama’a ya yi watsi da kiraye-kirayen da aka yi na a watsa kai tsaye a gidan talabijin kan yadda za a saurari tuhume-tuhume akan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a daidai lokacin da ta bayyana a gaban kwamitin da’a na majalisar bisa zargin rashin da’a a ranar Laraba.
Shugaban kwamitin, Sanata Neda Imasuen ya bayyana haka a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise News TV ‘The Morning Show’ wanda wakilinmu ya sanya wa ido.
- Matar Aure Ta Shiga Hannu Kan Zargin Kashe Kishiyarta A Bauchi
- Kotu Ta Ɗaure ‘Yan Tiktok 2 Kan Yaɗa Kalaman Batsa A Kano
Da yake bayyana matakin da kwamitin ya dauka, Imasuen ya jaddada bukatar ci gaba da mai da hankali kan lamarin da ke gaban kwamitin ba tare da raba hankali daga wani bangare na waje ba.
“A kan batun kafafen yada labarai, muna son mu yi taka-tsan-tsan don kada mu wuce gona da iri. Al’amari ne da ke cikin Majalisar Dattawa, kuma yin hakan ta hanyar kafafen yada labarai na iya daukar mana hankali. Zauren kwamitin zai iya ɗaukar mutane da yawa, kwamitin yana da mambobi kusan 23 ko 24. Muna son mu mai da hankali kan lamarin da ke gabanmu, kada wani lamari ya dauke mana hankali.”
Ya ba da tabbacin cewa za a yi wa Sanata Akpoti-Uduaghan adalci, inda ya ce: “Mai girma Sanata Natasha na da gata kamar kowane Sanata, kuma za a kare gatanta. Za ta samu adalci a wannan al’amari matukar ina wannan mukami. Kawata ce, kuma ba wanda zai taka mata hakkinta.”
Da yake karkare jawabinsa, Imasuen ya bukaci ‘yan Nijeriya da su kyale kwamitin ya gudanar da lamarin ba tare da matsi ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp