Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya musanta zargin cin zarafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a majalisa ta yi masa.
Da yake magana a zaman majalisae na ranar Laraba bayan hutun mako guda, Akpabio ya musanta zargin.
- Azumin Ramadan: Gwamna Buni Ya Amince Da Naira Miliyan 297 Don Ciyar Da Mutane 51,000 A Kullum
- An Bude Taron Shekara-shekara Na Majalisar Dokokin Kasar Sin
Ya bayyana cewa: “Ba zan taɓa cin zarafin wata mace ba. Mahaifiyata ta min tarbiyya mai kyau, kuma na kasance mai girmama mata koyaushe.
“Har lambar yabo na samu a matsayin gwamna mafi kishin mata a Najeriya.”
Ya roƙi ‘yan Nijeriya da kafafen yaɗa labarai da kada su yanke hukunci kafin kotu ta yanke nata.
Bayan wannan jawabi, Sanata Natasha ta gabatar da ƙorafi bisa dokar majalisar, imda ta zargi Akpabio da cin zarafinta da kuma amfani da matsayinsa ba daidai ba.
Ta kuma nemi izinin miƙa ƙorafin ga majalisar a hukumance.
Majalisar ta tura ƙorafin zuwa Kwamitin ladabtarwa domin ci gaba da bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp