Dakarun Sojin Nijeriya sun kashe aƙalla mayaƙan Boko Haram guda tara, ciki har da Amirul Bumma, wanda ya ƙware wajen ƙera bama-bamai a wani gumurzu da ya auku a dajin Sambisa, a Jihar Borno.
Wani masani kan tsaro, Zagazola Makama ne, ya bayyana hakan a ranar Laraba, yana mai cewa faɗan ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Bama yayin wani samame na musamman da dakarun sojin suka kai.
- Kwamitin Majalisa Ya Yi Watsi Da Ƙorafin Da Natasha Ta Shigar A Kan Akpabio
- Meranda Ta Yi Murabus, Obasa Ya Sake Zama Kakakin Majalisar Dokokin Legas
A cewarsa, sojoji daga Rundunar 21 Armoured Brigade, Rundunar 199 Special Forces, da kuma dakarun Civilian Joint Task Force, tare da wasu ƙungiyoyin tsaro, sun kai farmaki sansanin Boko Haram bayan samun bayanan sirri cewa mayaƙan na ƙoƙarin sake haɗuwa a wata mafaka kusa da Alai Dala Stand.
‘Yan ta’addan sun yi ƙoƙarin mayar da martani bayan an afka musu, amma sojojin sun yi nasarar fatattakar su da makamai.
Daga cikin manyan mayaƙan da aka kashe har da Amirul Bumma, wanda ke ƙera wa ƙungiyar bama-bamai, da sauran shugabanni kamar Bakura Ghana, Awari, Malam Kalli, Malam Usman Bula Kagoye, da Ibrahim Bula Abu Asma’u.
Sojojin sun kuma ƙwato makamai masu yawa.
Bayan artabun, Boko Haram sun yi yunƙurin kai farmakin ramuwar gayya ta hanyar birne bama-bamai a hanyoyin da sojojin za su bi.
Sai dai dakarun sun gano sama da guda 10 daga cikin abubuwan fashewar kuma sun tarwatsa su, wanda hakan ya hana aukuwar asarar rayuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp