Kungiyar kwadago ta kasa ta yi shirin yin zanga – zanga ta kasa baki daya saboda lamarin daya shafi karin kudin wutar lantarki da na kira, musamman ma kudin lantarkin da ake son a bar amfani da mafi arha /sauki da ake kira da suna (Band A).
Hakanne ya sa kungiyar ta yi kira da abokan gwagwarmayar su kasance cikin shirin kota- kwana na yin zanga- zanga da zata shafi kasa baki daya saboda karin kudin wutar lantarki dana kira.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 92, Sun Kubutar Da Mutane 75 A Cikin Mako Guda – DHQ
- Shugaban NAN:Muna Iya Ganin Basirar Sin Ta Manyan Taruka Biyu Da Take Gudanarwa Yanzu
An dauki shi matakin ne bayan taron da aka yi na Shugabannin kungyar a Yola hedikwatar Jihar Adamawa.
Halin da ake ciki dai yanzu ya nuna kungiyar ta yi shakkun idan gwamnatin tarayya za ta iya aiwatar da yarjeniyar da ta cimmawa da ita, da aka uyi ranar 25 ga watan Fabrairu 2025, lokacin da kwamitin mutum 10 wanda ya rage karin kudin da za a biya daga kashi 50 zuwa kashi 35.
Kungiyar kwadagon ta ja kunne inda ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba, matukar idan aka fara aikin da karin bai yi daidai da na kashi 35 ba, da take tsammani ba,za ta dauki matakin da ta yi niyyar.
Kungiyar ta yi tir da tsarin da hukumar kulawa wutar lantarki ta yi,wanda take neman ta ba masu amfani da wuta, nau’i- nau’in da suke ko ta kai su,ba domin komai ba don wata magana ta kara bunkasa samun wutar lantarki fiye da irin halin da ake ciki yanzu.
Kamar dai yadda kungiyar tace tsarin Hukumar wani kokari ne na karin kudin wutar lantarki na sauyawa masu amfani da wuta daga tsarin da suka saba amfani da shi mai sauki zuwa ga wanda zai kasance wanda yake mai tsada.
A sanarwar da aka fitar Shugaban kungiyar da Sakatarenta Kwamrade Joe Ajaero Komrade Emmanuel Ugboaja wadda ta ce tsarin da ake shirin yi tamkar “yin laifi ne ga tattalin arzikin kasa.”
Kungiyar NLC ta ga laifin ita hukumar NERC da ma’aikatar wutar lantarki da shirin gallazawa ‘yan Nijeriya wadanda suke rayuwa ta hannu baka- hannu kwarya.
Bugu da kari kungiyar ta kara da cewa muddin aka yi wani karin kudin wutar lantarki dana kira, hakan zai sa Talakawa sun yi zanga- zanga ta kasa baki daya. Domin kuwa ma’aikata da Talakawa ba za su iya hakurin irin tsaren tsaren takura na gwamnati ba.
Ga dai yadda sanarwar take: “Kwamitin zartarwa na kungiyar kwadago ya yanke shawarar daukar mataki idan aka kasa amfani matsayar da aka cimmawa ranar 1 ga Maris 2025, ba ayi hakan ba, ba tare da bata lokaci ba an sai kwamitin zartarwa na kasa da aka dorawa alhakin daukar mataki kamar dai lamarin yake abin yake a ranar10 ga Fabrairu 2025.
“Kan shirin komawa tsarin karin kudin wutar lantarkin, majalisar zartarwar kungiyar kwadago ta yi watsi da duk wani shirin da Hukumar (NERC), yadda ake neman tursasawa masu amfani da tsarin (B) su koma tsarin (A) a karkashin wani tsarin wayo da ake kiran shi domin a kara bunkasa samar da wutar lantarki, bayan kuwa maganar gaskiya ana shiri ne na gallazawa masu amfani da wutar lantarki.
“Tsarin shirin ma’aikatar wutar lantarki ba wani abu bane illa kamar kokarin da ake yi ne na gallazawa da takurawa Talakawa wadanda suke kokarin tafiyar da rayuwarsu cikin halin kunci.”
Daga karshe kwamitin zartarwa na kungiyar kwadago koda wane lokaci cikin shirin shi yake na kare al’umma daga duk wata irin takurawa, nuna fifiko,don haka ta yi kira ga dukkan kungiyoyin da suke karkashinta, da masu da’awar ci gaba, su zama a cikin shirin kota-kwana, na shiga zanga-zanga ko nuna rashin amincewa da duk wani tsari na kuntatawa na manufofi ko tsare-tsare masu takurawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp