Jami’an tsaro tare da haɗin gwuiwar ‘yan sa-kai sun kawar da fitaccen ɗan ta’addan Lakurawa, Maigemu, a jihar Kebbi.
Shugaban tsaro na jihar, Alhaji AbdulRahman Usman-Zagga, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a Birnin Kebbi, yana mai cewa an kashe Maigemu a ranar Alhamis a yankin Kuncin Baba na ƙaramar hukumar Arewa, bayan musayar wuta mai tsanani.
- Sojoji Sun Tarwatsa Sansanin Lakurawa A Sokoto Da Kebbi, Tare Da Ƙwato Makamai
- Babu Sauran Burbushin ‘Yan Ta’addan Lakurawa A Arewa Maso Yamma – Ministan Tsaro
Wannan nasara ta biyo bayan ziyarar da Gwamna Nasir Idris ya kai Bagiza da Rausa Kade makon da ya gabata, inda ya jajanta wa al’ummar da suka rasa ‘yan uwansu guda shida sakamakon hare-haren ɓarayin shanu na Lakurawa. Gwamnan ya yi alƙawarin ɗaukar matakan tsaro don daƙile miyagun ayyuka a yankin.
Usman-Zagga ya yaba wa gwamnan bisa jajircewarsa wajen tabbatar da tsaro da kuma samar da kayan aiki ga jami’an tsaro da ke gudanar da ayyuka na musamman a jihar.
Lakurawa wata ƙungiya ce ta ‘yan ta’adda da ta tsallako daga Jamhuriyar Nijar zuwa jihohin Sokoto da Kebbi, inda take haddasa rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp