Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya NPA, ta fara tattaunawa da Cibiyar Shirin Fadar Shugaban Kasa ta Samar Da Yanayin Kasuwanci a Saukake PEBEC domin samar da yanayin yin kasuwanci a cikin sauki, a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar
Manufar tattaunawar ita ce, domin samar da saukin yin kasuwanci a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar.
- Yadda Ake Ayyukan Gina Ababen More Rayuwa A Jihar Zamfara
- Shugaban NAN:Muna Iya Ganin Basirar Sin Ta Manyan Taruka Biyu Da Take Gudanarwa Yanzu
Shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya NPA Dakta Abubakar Dantsoho, ne ya jagoranci tawaga ta musamman zuwa Sakatariyar Cibiyar wadda Darakta Janar ta Cibiyar, Zahrah Mustapha Audu, ta tarbi tawagar.
Shugaban Hukumar Darakta Janar ta Cibiyar, tattaunawar da suka yi, sun mayar da hankali ne, kan yadda za a samar da saukin gudanar da kasuwanci a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar.
A lokacin ziyarar, sun kuma karkare kan yin hadaka a tsakanin NPA da Cibiyar, domin a samar da sakamako na gari, kan yin kasuwanci a cikin sauki.
A lokacin ganawar ta su, Dantsoho ya shedawa Daraktar yin ayyukan da ake gudanarwa a Hukumar ta Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa.
Da take mayar da jawabi Daraktar Janar ta Cibiyar ta bayyana tawagar ta NPA shawarar ta kan yadda za a kara inganta ayyukan NPA, musamman a bangaren samar da saukin yin kasuwanci, domin a kara habaka gasar yin kasuwanci da kuma kara tara kudaden shiga.
Kazalika, Hukumomin biyu, sun bayyana fatan kan hadakar a tsakaninsu, domin a samar da sauye-sauyen da a za su samar da sakamako mai kyau.
Hukumar ta NPA, ita ce aka dorawa nauyin tafiyarwa da kuma tafiyar da ayyukan Tashoshin Jirgen Ruwan Kasar.
Ana sa ran wannan hadakar a tsakanin NPA da PEBEC, za ta taimaka wajen samar da saukin kasuwanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp