Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) a Maiduguri, ta samu nasara cafke, Aisha Alkali Wakil, da aka fi sani da Maman Boko Haram, tare da Tahiru Saidu Daura da Prince Lawal Shoyede kan tuhume-tuhume uku da suka shafi damfara da satar kudin da ya kai naira miliyan 66.
Daya daga cikin tuhumar da ake musu da aka karanta a gaban Mai Shari’a, Aisha Kumaliya ta babbar kotun Maiduguri mai lamba 13.
Wadanda ake karar ana tuhumarsu da aikata laifuka daban-daban da suka hada da almundahana da zamba cikin aminci.
Wadanda ake kara na farko, na biyu da na uku kowannensu zai biya naira N3,750,000.00 ko zaman gidan yari na shekara biyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp