Kawo yanzu za a iya cewa wasanni za su kankama bayan da tun a ranar Juma’a, 5 ga watan Agustan 2022 aka fara buga wasannin gasar Premier League ta bana, kakar wasa ta 2022 zuwa 2023.
Idan mai karatu bai manta ba, a kakar da ta gabata kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ce ta lashe gasar, kuma biyu a jere da ta lashe wato a 2020 da 2021 da kuma ta 2021 da 2022 a karkashin mai koyarwa Pep Guardiola Sai dai wani sauyi da aka samu a kakar wasa ta bana ta 2022 zuwa 2023, kungiyoyi za su iya sauya ‘yan wasa biyar maimakon uku da ake yi a baya kuma za’a iya sauya ‘yan wasa uku a minti 45 din farko, sannan a saka sauran a zagaye na biyu, domin a rage bata lokaci idan ana buga wasa.
- 2023: Ko Yawan Masu Rajistar Zabe Zai Iya Tasiri Ga ‘Yan Takara?
- Wike Ga Atiku : Kar Ka Zarge Ni In Ka Fadi A Zabe
Sannan wannan shi ne karon farko da za’a fara canja ‘yan kwallo biyar a gasar Premier League, bayan da tuni Bundesliga da Ligue 1 da Primeir Liga da La Liga da kuma Serie A suka dade da irin wannan tsarin.
Haka kuma a kakar nan za’a buga gasar kofin duniya da kasar Katar za ta karbi bakunci tsakanin watan Nuwamba zuwa cikin watan Disamba saboda haka za’a yi hutu a Premier a mako na12 ko na 13 ga watan Nuwamba zuwa 26 ga watan Disambar, domin gasar ta cin kofin duniya.
Har ila yau, wani canji da aka samu shi ne kyaftin-kyaftin din kungiyoyin Premier League sun amince cewar ba duk wasa ne za su ci gaba da sa gwiwa daya a kasa ba daga kakar nan, domin goyon bayan yaki da wariwar launin fata.
An dai amince cewa za’a iya yi a farkon bude gasar ko lokacin rufe ta ko wani babban wasa a Ingila, shima ba wai ya zama wajibi ba sai dai kuma kungiyoyin sun yi kira da babbar murya cewar suna yaki da wariyar launin fata da duk wani nau’in cin zarafi a fannin kwallon kafa.
Kamar yadda aka sani kungiyoyi 20 ne suke buga gasar Premier League, inda 17 daga bara za su hadu da ukun da suka samu gurbin fafatawa a kakar bana daga Championship kuma wadanda suka hauro zuwa Premier League sun hada da Fulham, wadda ta yi kaka daya rabonta da gasar da Bournemouth kaka biyu rabonta da wasannin da Nottingham Forest, wadda shekara 23 rabonta da Premier League.
Gibin shekara 23 rabon da kungiya ta koma buga Premier League da Nottingham ta yi shi ne har yanzu mai tsawo a tarihi da ake da shi, bayan barin gasar kuma kungiyoyi ukun sun maye gurbin Burnley, wadda ta yi kakar wasa shida a Premier League da Watford da kuma Norwich City, wadanda suka yi kaka daya a wasannin da aka karkare a bara.
Da yake ranar 5 ga watan Agusta aka fara kakar wasan Premier League ta 2022/23, inda aka fara da kece raini tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace da Arsenal a filin wasa na Selhust Park dake birnin Landan, Arsenal ce ta samu nasara da ci 2-1.
Tuni kungiyoyi 20 da za su fafata a kakar bana suka daura aniyar yadda za su taka rawar gani a babbar gasar ta Ingila ta bana domin tuni wasu da dama sun sayo sababbin ‘yan wasa domin kara bunkasa kwazonsu, yayin da wasu suka buga wasannin sada zumunta.
A bana Nottingham Forest wadda rabon da ta buga Premier League tun bayan shekara 23, ita ce kan gaba da ta dauki ‘yan kwallo 13 kawo wannan lokacin sai dai ita kuwa Leicester City kawo yanzu ba ta sayi dan kwallo ko daya ba, watakila ta dauka nan gaba.
Kungiyoyin Manchester City da Liberpool su ne wadanda ake ganin kamar sun yi ciniki mai kyau ganin yadda City, wadda ita ce mai kare kambu ta dauki dan wasa Erling Haaland ita kuwa Liberpool Darwin Nunez ta dauka daga Benfica.
Duka kungiyoyin da suke buga gasar dai sun yi iya yinsu wajen ganin sun kara karfi domin tunkarar wannan kakar da za’a shiga sati na biyu a gobe, sai dai abin tambayar a nan shi ne wacce kungiya ce za ta lashe gasar ta bana?