• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadin Gwiwar Sin Da Nijeriya Za Ta Ba Mata Damar Cimma Burikansu

by CGTN Hausa and Sulaiman
8 months ago
Sin

LABARAI MASU NASABA

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijeriya, ya shirya taro domin bikin ranar mata ta duniya da ake gudanarwa a ranar 8 na watan Maris din kowacce shekara. Taron mai taken “Labarinta, Makomarta” wanda ya gudana ranar Juma’a a cibiyar raya al’adu ta kasar Sin dake birnin Abujan Nijeriya, ya hada mata daga dukkan bangarorin rayuwa, inda suka yi waiwaye kan ci gaban da suka samu da ma tsara hanyar tabbatar da daidaiton jinsi.  

Da yake jawabi yayin taron, jakadan Sin a Nijeriya Yu Dunhai, ya nanata muhimmancin bikin na wannan shekara kasancewar ya zo daidai da cikar Yarjejeniyar Beijing ta tabbatar da daidaiton jinsi ta MDD, shekaru 30 da kulluwa.

  • A Mai Da Duniya Ta Zama Ta Kasa Da Kasa
  • Shugabannin Larabawa Sun Amince Da Tsarin Gina Gaza Da Zai Lakume Dala Biliyan 53

Ya kara da cewa, “Sin za ta hada hannu da Nijeriya wajen kyautata aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da aiwatar da shirye-shiryen hadin gwiwa 10 dake tsakaninsu, ciki har da inganta musaya tsakanin mata da hada hannu wajen gina al’ummar Sin da Nijeriya mai makoma ta bai daya. Ya kara da cewa, ya yi imani mata da dama za su amfana tare da cimma burikansu da samar da kyakkyawar makoma ta hanyar ingantaccen hadin gwiwar Sin da Nijeriya, karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.

A nasa jawabi, mukaddashin babban sakataren ma’aikatar raya al’adu da fasahohi da bude ido da tattalin arzikin bangaren, Oraeluno Rapheal, ya kara tabbatar da goyon bayan da gwamnatin kasar ke bayarwa ga ci gaban harkokin mata. Ya ce Nijeriya za ta ci gaba da tabbatar da inganta kwarewar mata ta hanyar bayar da horo da musayar al’adu da sauran shirye-shiryen dake da zummar ba mata damar kara taka rawar gani. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo
Daga Birnin Sin

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
Next Post
Kasar Sin Za Ta Kara Albarkatu Da Kudade Domin Tallafawa Samar Da Ayyukan Yi

Kasar Sin Za Ta Kara Albarkatu Da Kudade Domin Tallafawa Samar Da Ayyukan Yi

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

November 7, 2025
GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

November 7, 2025
Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

November 7, 2025
Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

November 7, 2025
Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

November 7, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

November 7, 2025
An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.