Shugabannin kasashen Larabawa sun amince da tsarin sake gina Gaza wanda zai lakume kudi da ya kai dala biliyan 53 wanda ya sha bamban da manufar Trump na son “karbe iko da Gaza” da kuma fitar da Falasdinawa sama da miliyan biyu daga yankin.
Sun amince da tsarin ne a wani taron gaggawa da suka gudanar a Alkahira, babban birnin Masar.
- Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [1]
- Nijeriya Za Ta Nuna Gyare-gyaren Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu A Taron Kasuwanci A Faransa
“Tsarin Masar a yanzu shi ne tsarin Larabawa,” kamar yadda sakatare-janar na kungiyar kasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit bayan kammala zama na tsawon sa’o’i da aka yi.
Ba tare yin magana kan manufar shugaba Trump a kan Gaza ba, ya bayyana cewa “matsayar Larabawa ita ce watsi da duk wani yunkuri na daidaita Falasdinawa, ko da da son su ko tilasta su”.
Masar ta fitar da wani jadawali mai shafi 91 ciki har da hotuna na yadda birnin Gaza zai kasance idan aka sake gina shi, wanda ya yi sabani da tsarin Amurka mai suna “Sake Mayar da Gabas Ta Tsakiya” wanda ya kada kasashen Larabawa da kuma duniya.
Abin da ya sa wannan tsari ya yi daban shi ne ba wai domin irin tsarin gine-gine da za a yi ba; akwai allunan batun siyasa da kuma ‘yancin Falasdinawa.
A jawabinsa a wajen taron, shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya yi kira da a samar da tsare-tsare guda biyu da za su tafi lokaci daya wanda aka fi sani da tsarin kasa biyu – kasar Falasdinawa da kuma ta Isra’ila.
Larabawa da kuma sauran mutane na ganin wannan itace kadai hanyar samar da mafita ga rikicin da aka dade ana fama da shi, sai dai Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kawayensa sun yi watsi da batun.
Wannan sabon tsari ya bayyana cewa Gaza za ta zauna karkashin kulawar “gwamnatin Falasdinawa na wucin-gadi” wanda ya kunshi kwararru.
Sai dai ba su bayar da cikakkun bayanai ba kan rawar da har ma idan akwai wanda Hamas za ta taka.
A kann batun barazanar kungiyoyin mayaka, kungiyar ta ce za a warware wannan matsala idan aka magance abin da yake janyo rikicin daga bangaren Isra’ila.
Yayin da wasu kasashen Larabawa ke yin kira don kawo karshen Hamas; saura kuma sun yi imanin cewa matakin haka ya rage ga Falasdinawa.
An bayyana cewa Hamas ta ce ta amince ba za ta taka wata rawa ba wajen tafiyar da Gaza, amma sun bayyana karara cewa ajiye makamai ba abu ne mai yiwuwa ba.
Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya yaba da tsarin shugaba Trump kan Gaza, ya sha bayyana cewa Hamas ba ta da wata rawa da za ta taka, har ma da hukumomin Falasdinawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp