An yi cikakken zama na uku na taron shekara shekara na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin da safiyar yau Lahadi a babban dakin taron al’umma dake birnin Beijing, inda zaunannen memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar, wanda kuma shi ne shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin, Wang Huning ya halarci taron, kana, membobin majalisar guda 14 ne suka gabatar da jawabai.
A jawabinta, mambar majalisar Ge Huijun ta ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi a wajen babban taron murnar cika shekaru 75 da kafa majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar, jawabin da ya kafa alkabila da samar da babban tushe ga ci gaban harkokin majalisar. Ta ce ya dace membobin majalisar su kara gogewa wajen sauke nauyin aiki, da kara kwarewa a fannonin da suka shafi bada jagoranci ta fuskar siyasa, da bada shawarwari game da ayyukan zamanantar da kasa, da kara tuntuba gami da hidimtawa jama’a, tare kuma da kokarin raya kasa da farfado da al’ummomin kasar. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp