Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), Archbishop Daniel Okoh, ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya na fama da yunwa da rashin tsaro a ƙarƙashin mulkin Shugaba Bola Tinubu.
Da yake jawabi a taron Catholic Bishops’ Conference of Nigeria a Abuja, Okoh ya buƙaci ayi gaggawar ɗaukar mataki domin rage matsalolin da ya bayyana a matsayin “zalunci” a ƙasar. Ya ce matsalolin yunwa, da talauci, da rashin tsaro da cututtuka sun sa wasu ‘yan ƙasa sun fidda rai ga samun adalci gaba ɗaya.
- Rufe Makarantu A Ramadan Ya Tauye Ƴancin Ɗalibai – CAN
- Nijeriya Za Ta Nuna Gyare-gyaren Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu A Taron Kasuwanci A Faransa
Ya jaddada cewa lokaci ya yi da za a koma ga Allah tare da sake duba dangantakar da ke tsakanin ‘yan Nijeriya da junansu.
Okoh ya bayyana cewa ta hanyar ƙoƙarin cocina na kare gaskiya da adalci, na taka rawa wajen kawo sauyi mai kyau a Nijeriya. Ya ce idan ‘yan ƙasa suka haɗa kai, za a iya samun ƙasar da ke cike da ƙauna, da zaman lafiya, da ci gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp