Aƙalla mutum 1,010 ne suka mutu a faɗin Nijeriya sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da na jami’an tsaro a watan Fabrairu, kamar yadda rahoton kamfanin Beacon Security and Intelligence ya bayyana.
Rahoton ya nuna cewa an samu raguwar sace mutane daga 1,101 a watan Janairu zuwa 955 a Fabrairu, amma adadin mutanen da aka kashe ya ƙaru daga 991 zuwa 1,010.
- Barcelona Ta Tsallaka Zuwa Matakin Kwata Fainal A Gasar Zakarun TuraiÂ
- Majalisar Dokokin Kasar Sin Ta Rufe Zaman Taronta Na Shekara-shekara
Daga ranar 1 zuwa 28 ga watan Fabrairu, an samu hare-hare da tashin hankali har 716, waÉ—anda suka haddasa satar mutane 955.
Binciken ya kuma nuna cewa mutum 592 daga cikin waɗanda suka mutu fararen hula ne, inda ‘yan bindiga suka fi kai mafi yawan hare-hare 478, yayin da jami’an tsaro suka haddasa 177.
Jihohin da suka fi fama da hare-haren sun haÉ—a da Katsina, Kaduna, Neja, Zamfara, Sakkwato, Borno, da Kebbi.
Duk da raguwar hare-haren da kashi 2.19 idan aka kwatanta da Janairu, har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da zama barazana ga al’umma a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp