Fc Barcelona ta samu damar tsallakawa zuwa matakin kwata fainal na gasar Zakarun Turai ta bana, ta samu wannan nasarar ne bayan samun galaba a kan kungiyar Benfica a filin wasa na Luis Companys da ke Birnin Barcelona.
A wasan farko da Barcelona ta ziyarci Benfica an tashi wasan da ci 1-0, amma kuma wasan yau da aka buga a gidan Barcelona, masu masaukin bakin sun zazzagawa Benefica kwallaye uku rigis a raga.
- Dalilin Da Ya Sa Aka Soke Wasan Barcelona Da Osasuna
- EFCC Ta Kama ‘Yan China 4, Da Wasu Mutum 27 Kan Zargin Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Jos
Lamine Yamal da Raphinha da ya jefa kwallo biyu ne su ka jefawa Barcelona kwallayenta, inda Nicolas Otamendi ya farkewa bakin kwallo daya a minti na 14.
Da wannan nasarar ne Barcelona ta samu nasarar zamowa kungiya ta farko da ta tsallaka zuwa matakin kwata fainal a sabon jadawalin gasar Zakarun Turai da aka fara amfani da shi bana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp