Sandeep Chaturbedi, mai shekara 26, na shirin yin sabuwar wakarsa a wani dakin rera wakoki da ke birnin Ayadhya a Jihar Uttar Pradesh da ke Arewacin Indiya.
Wakar da yake rerawa kan masallaci ne da ya zama abin ce-ce-ku-ce bayan mabiya addinin Hindu sun yi ikirarin cewa suke da hakkin bauta a yanki.
- Martanin El-Rufa’i: Ko Gawata Ba Za Ta Kusanci PDP Ba
- “Korar Fulani A Edo: Ina Ake So Wadanda Aka Haifa A Jihar Shekara 50 Su Koma?”
Wakar na dauke da baituka kan wariyar da ake nuna wa Musulmai.
Amma Chaturbedi na cewa wakar za ta sake farfado da fannin nishadi.
Yayin da mutane ke iya cin karensu ba babbaka da kalaman kiyayya a Indiya, baitin waka na tattare da cin mutunci da barazana.
Suna yin kalaman kiyayya ne bisa tunanin cewa masu bin addinin Hindu sun sha bakar wahala a tsawon daruruwan shekaru a don haka yanzu lokacin ramuwa ne.
Masu rubuce-rubuce da sharhi kan siyasa irin su Nilanjan Mukhopadhyay sun ce baya ga batun samar da kudaden shiga, irin wadannan wakoki na jan hankali kan mawaka.
Amma a wurinsa, wannan ba waka ba ce. “Wannan kira ne na yaki.
Kamar ana son amfani da waka ne domin nasarar yaki.
Wannan rashin sanin dacewa ne a fannin waka kuma an kwashe shekaru da dama ana yin hakan.”
Chaturbedi ya soma waka da wakokin bege shekaru 10 da suka gabata, amma ya sauya salo ‘yan shekarun baya lokacin da ya yanke shawarar soma wakokin bautar “Hindu da na hadin-kan kasa”.