Ukraine ta amince da dakatar da yaƙi na tsawon wata guda da Rasha, bayan shafe shekaru uku suna gwabzawa.
Wannan mataki ya biyo bayan tattaunawar da wakilan Ukraine ke yi da Amurka a birnin Jeddah, Saudiyya.
- Yawan Bishiyoyin Da Aka Dasa A Kasan Kasar Sin Ya Kai Kashi 25%
- Muddin Nahiyar Afirka Ta Farka Ba Za A Iya Raina Ta Ba
Amurka ta jinjina wa wannan mataki tare da sanar da dawo da yarjejeniyar musayar bayanan sirri tsakaninta da Ukraine.
Wannan yarjejeniya ce da Donald Trump ya dakatar a makon jiya bayan saɓanin da ya shiga tsakaninsa da shugaba Volodymyr Zelensky.
A halin yanzu, ana shirin miƙa wa Rasha takardar matsayar da aka cimma a taron Jeddah domin nazari da yiwuwar amincewa da ita.
Majiyoyi sun bayyana cewa Donald Trump na shirin tattaunawa da Vladimir Putin a cikin makon nan domin ƙara fahimtar juna dangane da wannan shiri.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, na kira ga ƙasashen Turai da su haɗa kai domin tallafa wa Ukraine wajen tabbatar da tsaron ƙasar bayan wannan tsagaita wuta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp