Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya bai wa jami’an tsaro karin motocin sintiri (HILUX) hudu domin inganta harkokin tsaro a fadin Jihar.
Gwamnan, wanda ya samu wakilcin babban sakatare na fadar Gwamnatin Jihar, Alhaji Dahiru Zaki, ya yaba wa jami’an tsaron kan gudummawar da suke bayar wa na kariyar rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar.
- 2027: Na Shirya Tsaf Don Yin Aiki Tare Da Peter Obi Don Ceto Ƙasar Nan, Gwamnan Bauchi
- Tabbaci Kan Bunkasuwar Tattalin Arziki Mai Dorewa A SinTabbaci Kan Bunkasuwar Tattalin Arziki Mai Dorewa A Sin
Gwamna Idris ya tabbatar da kudurin gwamnatinsa na ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro da ke jihar.
Motocin dai, an bai rundunar soji Uku, yayin da rundunar ‘yansanda ta Mopol ta karbi daya. Kwamandan Barikin Soji na Birnin Kebbi, Manjo A. P. Azubuine, ya bayyana godiyarsa na goyon baya da gwamnatin ke basu wajen yaki da ‘yan ta’adda a fadin jihar.
Shi ma a nasa bangaren, ACP Aliyu Jega, kwamanda Mopol 36 da ke Birnin Kebbi, ya mika godiyarsa ga gwamnan, inda ya kara da cewa, Motar za ta taimaka musu wurin sauke nauyin da ya rataya akansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp