Bayan shekara ɗaya ba tare da kiran tawagar ƙasar Ingila ba, an saka sunan Marcus Rashford, ɗan wasan gaba na Manchester United da ke zaman aro a Aston Villa, a cikin sabuwar tawagar da sabon koci Thomas Tuchel zai jagoranta.
Wasan ƙarshe da Rashford ya buga wa Ingila shi ne sada zumunci da Brazil a watan Maris 2024.
- Birnin Beijing Ya Shirya Yiwa ‘Yan Mata Rigakafin Cutar HPV Kyauta
- Dangote Da NNPCL Sun Koma Teburin Tattaunawa Kan Cinikin Danyen Mai A Kan Naira
Tun bayan komawarsa Villa a matsayin aro daga Manchester United a watan Janairu, ya yi ƙoƙari sosai, duk da cewa bai ci ƙwallo ba, ya taimaka an zura huɗu.
Baya ga Rashford, akwai Dan Burn na Newcastle da Myles Lewis-Skelly na Arsenal, waɗanda suka samu kiran farko zuwa tawagar Ingila.
Ingila za ta fara neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na 2026 da wasanni a Wembley da Albania da Latvia a ranar Juma’a 21 da Litinin 24 ga Maris.
Rashford, mai shekaru 27, ya buga wa Ingila wasanni 60 tare da cin ƙwallaye takwas.
Amma bai samu dama a hannun tsohon koci Gareth Southgate ba, inda aka cire shi daga gasar Euro 2024 da kuma Nations League ta 2024-25.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp