A cikin makon da ya gabata ne mataimakin Shugaban kungiyar manoma shinkafa ta jihar Kaduna Alhaji Hassan Tahir ya bukaci dukanin manoman da suka amfana da duk wani tallafin bashi da suka samu, da su dawo da basussukan da suka karba ta hanun kungiyoyin da suka karba batare da ankai ruwa rana da suba.
Mataimakin shugaban ya yi wannan kiranne a yayin wata ziyara da wakilin mu ya kai masa a ofishinsa dake sabuwar randar Kano dake Kwangila Zariya.
- Obasanjo Ya Roki Marayun Borno Su Yafe Wa ‘Yan Ta’addar Da Suka Kashe Iyayensu
- Yadda Mai Wanke-wanke Ta Zama Mataimakiyar Shugaban kasa
Sakamakon irin wannan dabi’ar da wasu manoma suka nunane gwamnati a bana ta janye tallafin da take badawa, domin manoman su fahimci irin gagarumin gudun mowar da take badawa wajen aikin gona, sakamakon haka yau manomi yana sayen taki a hannun yan Kasuwa sama da Dubu 25.
Alhaji Hassan Tahir ya ce babban abin da yafi basu mamaki shine, bawai da kudi aka ce a biya wannan bashinba da amfanin da manomi ya samune zai biya amman sai mtum yaki biya har sai andaukar masa mataki na cin zarafi, wanda hakan bai dace ba