• Leadership Hausa
Thursday, March 23, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Mai Wanke-wanke Ta Zama Mataimakiyar Shugaban kasa

by Rabi'u Ali Indabawa
7 months ago
in Al'ajabi
0
Yadda Mai Wanke-wanke Ta Zama Mataimakiyar Shugaban kasa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Sakamakon zaben Shugaban kasar Kolombiya na 2022 ya kasance na ban mamaki saboda dalilai da dama, tsohon dan gwagwarmaya Gustabo Petro ya zama shugaban kasa na farko mai ra’ayin kawo sauyi kuma abokiyar takararsa ita ma ta kafa tarihi.

A ranar 7 ga Agusta, Francia Markuez, wadda matashiya ce kuma uwa, wacce a da ta kasance kuyanga da mai hakar zinare, ta zama mataimakiyar shugaban kasa bakar fata ta farko a Kolombiya.

  • Kotu Ta Daure Fasto Da Wasu 2 Kan Zargin Yin Sojan Gona Da Sunan Jami’an EFCC, ICPC A Akwa Ibom
  • Gwamnatin Katsina Ta Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira 12,000 Zuwa Matsugunansu- Shugaba 

Markuez, mai shekaru 40, tana da kwarjini na musamman idan aka kwatanta ta da duk magabatanta.

Da farko, ba ta cikin tsarin siyasa da zamantakewar Kolombiya.

Kolombiya kasa ce mai kabilu da al’adu daban-daban kuma a al’adance ma’aikatunta sun kasance a hannun mazajen birnin, masu arziki kuma farar fata.

Labarai Masu Nasaba

Tarihin Mamayar Tattar II

Bayani A Kan Starlink, Da Yadda Tsarinsa Ya Ke (Kimiyya)

Amma sabuwar mataimakiyyar shugaban kasa ba ta gamsu da kimar kasancewa mace bakar fata ta farko da za ta hau karagar mulki a karon farko ba.

Yaki da talauci da kuma tafiya da kowa da kowaTa shaida wa manema labarai a wata hira da aka yi da ita a ranar 23 ga watan Yuni cewa “Ba wai na kawo kaina ba ne don na nuna fuskata a matsayinbakar fata ko na nuna kaina a matsayin mace ko kuma kawai na nuna cewa gwamnatinmu ta kunshi kowa da kowa a’a”.

An haifi Markuez a Yolombo, wani kauye mai nisan kilomita 437 daga Bogota babban birnin kasar.

Kauyen na cikin Jihar Cauca daya daga cikin yankuna masu fama da talauci da kuma yawan kauyuka a kasar.

Haka zakalika rikicin da aka shafe tsawon shekaru 65 ana yi tsakanin gwamnati da kungiyoyin sa kai da ‘yan tawaye ya shafi yankin Cauca sosai.”Alal misali an yi watsi da al’ummata na tsawon lokaci,” in ji ta. “Babu ruwan sha da tsaftar muhali ko wutar lantarki.”

Yadda ta zama uwa da mai hakar ma’adinai kuma ‘yar gwagwarmaya

Markuez tana daya daga cikin yara 12 kuma ta yi rayuwa a shekarunta na farko ta hanyar yin aiki tare da iyayenta a wata mahakar zinare da ke bakin kogin Obejas.

Tana da shekaru 16 ta haihu kuma ta fara aiki a matsayin ‘yar aikin gida da ke wanke-wanke da sauran ayyuka, domin ta samu kudin kula da babban danta Carlos tare da biyan kudin karatu a Jami’a a fannin aikin noma, tana kuma da Digirin Digirgir da ta samu shekaru biyu da suka gabata a fannin aikin lauya.

Markuez ta kuma rika fafitukar kare muhalli, ciki har da zanga-zangar nuna adawa da shirin karkatar da kogin Obejas zuwa madatsar ruwan Salbajina a cikin shekarun 1990. Tana cikin wadanda suka rika gangamin da ya sa Kotun kolin kasar ta dakatar da aikin.

Daga bisani ta jagoranci wasu da suka nuna turjiya a kan shirin gwamnatin tarayya na ba kamfanonin kasashen waje hakkin hako ma’adinai bayan ta kori bakar fata ‘yan Kolombiya da suka mallaki filayen hakar ma’adinai.

A 2014 tauraruwar Markuez ta haskaka inda ta jagoranci mata da dama a wani tattaki mai nisan kilomita 350 zuwa Bogota domin neman daukar mataki matsalolin da ake fuskanta a fannin zamantakewa da muhalli da hakar ma’adinai ba bisa kai’da ba a Cauca a lokacin mulkin Shugaba Juan Manuel Santos.

Markuez ta kuma halarci tattaunawar zaman lafiya tsakanin gwamnatin tarayya da FARC, wadda ita ce babbar kungiyar ‘yan tawayen Kolombiya.

A yayin tattaunawar, ta bayar da hujjar cewa ‘bakar fata ‘yan Kolombiya sun shafe shekaru da dama suna wahala sakamakon wannan rikici.

“Bayanai daga ma’aikatar kididdiga ta kasa sun ce mata bakar fata suna rayuwa a matsakaicin shekaru biyar kasa da sauran matan Kolombiya.

Ina tsammanin wannan ita ce shaida a kan yadda tsarin wariyar launin fata yake aiki,” in ji ta a cikin hirar 23 ga Yuni.

Ta rika fuskantar barazanar mutuwa A 2018, an ba Markuez lambar yabo ta muhalli ta Goldman, wadda aka sani da sunan “Kyautar Nobel ta Green”.

Sai dai kuma wannan babban matsayi ya nuna cewa nan gaba mataimakiyyar shugaban kasar za ta fuskanci barazana a kasar da ta yi kaurin suna wajen kashe masu rajin kare hakkin bil’adama.

A cikin 2021 kadai, an kashe mutum 138 daga cikinsu a Kolombiya a cewar wata kungiyar farar hula da ake kira Front Line Defenders, watau kashi daya bisa uku na kashe-kashen da aka yi wa rajista a duk duniya a wannan shekarar.

Markuez ta tsallake rijiya da baya a shekarar 2019, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari wani taron da ta halarta a birnin Santander de kuilichao na Cauca.

Maimakon ta tsoratar da Markuez, lamarin da ya yi kamar ya sa ta himmatu wajen fafutukar ganin an yi adalci.

Ta sanar da takararta ta shugaban kasa a watan Afrilun 2021 kuma ta sami tagomashi da ya sa ta kai matsayi na biyu a zaben fitar da gwani na gammayar jam’iyyu masu ra’ayin kawo sauyi .

Wanda ya yi nasara shi ne Gustabo Petro, wanda nan take ya gayyaci Markuez don yin takara a matsayin mataimakiyyarsa.

“Gayyatar da muke yi, watau ni da Gustabo Petro , ita ce babbar yarjejeniya kasa wadda ta kafa tushe mai karfi da fifiko don ci gaba da samar da zaman lafiya mai dorewa da sulhu da kuma adalci na zamantakewa,” in ji Markuez.

Kalubalen dake gabansu a yanzu shi ne cika alkawuran da aka yi wa ‘yan kasar Kolombiya wadanda sun fidda rai daga tsarin zaben kasar wadanda kuma ba su da gata kamar yadda Markuez ta bayyana su a cikin jawaban yakin neman zabenta.

Ga masu lura da al’amura, cika wadannan alkaura wani jan aiki ne mai cike da kalubale kamar yadda Markuez ta fuskanta har ta zama mataimakiyyar shugaban kasa.

“Ina ganin na fito fili karara don na nuna wa al’ummar kasar, da jama’ata, ba za mu iya sauya matsalolin da suka faru a cikin shekaru 500 da suka gabata ba a shekaru hudu kacal,” in ji ta.

“(Amma) dole ne mu shirya a matsayinmu na kasa don kawo ci gaba gwargwadon iyawarmu.”

Mutane kalilan ne za su yi nuna shakkun cewa Markuez tana da kuzarin wannan gwagwarmaya.

Tags: 'Yar Wanke-WankeAbokiyar TakaraAl'ajabiKolombiyaShugaban KasaZabe
ShareTweetSendShare
Previous Post

Gwamna Wike Ya Karyata Batun Maka Atiku Da Tambuwal A Kotu

Next Post

Rashin Shugabaci Nagari Ya Jefa Nijeriya Halin Da Take Ciki, In Ji SDP

Related

Tarihin Mamayar Tattar II
Al'ajabi

Tarihin Mamayar Tattar II

2 weeks ago
Bayani A Kan Starlink, Da Yadda Tsarinsa Ya Ke (Kimiyya)
Al'ajabi

Bayani A Kan Starlink, Da Yadda Tsarinsa Ya Ke (Kimiyya)

3 weeks ago
Zaben 2023: Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC 3 A Taraba
Al'ajabi

Zaben 2023: Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC 3 A Taraba

4 weeks ago
Mai Juna Biyu Ta Rasu A Rumfar Zabe A Jihar Zamfara
Al'ajabi

Mai Juna Biyu Ta Rasu A Rumfar Zabe A Jihar Zamfara

4 weeks ago
‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutum 3 Kan Zargin Mallakar Kudaden Jabu A Jihar Kebbi
Al'ajabi

‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutum 3 Kan Zargin Mallakar Kudaden Jabu A Jihar Kebbi

1 month ago
Fasto Ya Mutu A Kokarin Yin Azumin Kwana 40
Al'ajabi

Fasto Ya Mutu A Kokarin Yin Azumin Kwana 40

1 month ago
Next Post
Rashin Shugabaci Nagari Ya Jefa Nijeriya Halin Da Take Ciki, In Ji SDP

Rashin Shugabaci Nagari Ya Jefa Nijeriya Halin Da Take Ciki, In Ji SDP

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Dokokin Kogi Ta Dakatar Da ‘Yan Majalisa 9 D Wasu Kan Zargin Ta’addanci

Majalisar Dokokin Kogi Ta Dakatar Da ‘Yan Majalisa 9 D Wasu Kan Zargin Ta’addanci

March 23, 2023
An Yaba Da Yadda Tawagar Likitocin Kasar Sin Ta Ba Da Hidimar Kiwon Lafiya A Sudan Ta Kudu

An Yaba Da Yadda Tawagar Likitocin Kasar Sin Ta Ba Da Hidimar Kiwon Lafiya A Sudan Ta Kudu

March 23, 2023
Xi Jinping Ya Kammala Ziyararsa A Kasar Rasha Cikin Nasara

Xi Jinping Ya Kammala Ziyararsa A Kasar Rasha Cikin Nasara

March 23, 2023
Matawalle Ya Karbi Faduwa, Ya Yi Fatan Alheri Ga Sabon Gwamnan Zamfara

Matawalle Ya Karbi Faduwa, Ya Yi Fatan Alheri Ga Sabon Gwamnan Zamfara

March 23, 2023
Siyasantar Da Batun Gano Asalin COVID-19 Dabara Ce Ta Boye Gaskiya

Siyasantar Da Batun Gano Asalin COVID-19 Dabara Ce Ta Boye Gaskiya

March 23, 2023
Jirgin Saman Nijeriya Zai Fara Aiki Kafin Ranar 29 Ga Mayu

Jirgin Saman Nijeriya Zai Fara Aiki Kafin Ranar 29 Ga Mayu

March 23, 2023
Ina So A Ko’ina A Ji Hikima Da Fasaharmu – Yusuf King

Ina So A Ko’ina A Ji Hikima Da Fasaharmu – Yusuf King

March 23, 2023
Hadin Gwiwar Sin Da Rasha Na Da Muhimmanci Sosai Ga Duniya

Hadin Gwiwar Sin Da Rasha Na Da Muhimmanci Sosai Ga Duniya

March 23, 2023
Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumin Gobe A Wasu Birane

Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumin Gobe A Wasu Birane

March 23, 2023
Gyare-gyare Su Kan Faru Ne Bisa Sauyawar Tunanin Mutum

Gyare-gyare Su Kan Faru Ne Bisa Sauyawar Tunanin Mutum

March 23, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.