Tsohon gwamnan Jihar Jigawa kuma kusa a jam’iyyar PDP, Sule Lamido ya yi watsi da kiran da tsohon gwamnan Jihar Kaduna. Malam Nasir El-Rufa’i ya yi wa shugabannin adawa da su shiga jam’iyyar SDP. Ya ce El-Rufa’i ya yi kadan ya sa su bar jam’iyyar PDP.
El-Rufa’i, wanda a kwanan nan ne ya bar jam’iyyar APC zuwa SPD, ya bukaci manyan ‘yan siyasa ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi su shiga jam’iyyar tare da shi.
Sai dai kuma Lamido wanda ya kasance abokin Atiku na kusa, ya soki wannan gayyatar da El-Rufa’i ya yi musu, sannan ya kalubalanci tsarin tafiyar siyasar El-Rufa’i tare da yin alkawarin ci gaba da kokarin tallafa wa al’umma.
- Bukatar Kawo Karshen Karin Kudin Kiran Waya Da Na Data
- Majalisar Dokokin Nijeriya Ta Zama Ƴar Amshin Shata — Kwankwaso
“Idan ba rashin kunya ba, ta yaya zai iya kalle mu a PDP kuma ya ce mu shiga wata jam’iyya. PDP wadda muka gina, ta haife shi a siyasa. Ta yaya jika zai kalli kakansa ya ce masa bai son komi ba?,” in ji Lamido.
Ya kuma kalubalanci da’awar El-Rufai na cewa yana kaunar Nijeriya fiye da wasu. Shin shi nr kawai mai son Nijeriya? Kana nufin mu babu Nijeriya a cikin zukatanmu ne?.”
Lamido ya tuna kalamun El-Rufai na cewa babu dattawan siyasa a Nijeriya, amma kuma ya garzaya wurin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya saka masa albarka lokacin da zai bai APC. Ya ce idan har ya tsaya da kafafuwansa, me ya sa ya tafi wurin Buhari?
Lamido ya kasance tsohon sakataren jam’iyyar SDP, ya sake jaddada alkawarinsa ga PDP, yana mai cewa bai ga dalilin barinsa jam’iyyar ba.
Lokacin da na kasance sakataren jam’iyyar SDP, ina El-Rufai yake? Ina Shehu Gabam, shugaban jam’iyyar na kasa na yanzu? Duk da kalubalen da PDP ke fuskanta, a nan ne aka haife shi a siyasa. Idan yana ikirarin cewa PDP ta mutu, to ya manta da asalinsa.”
Yana jaddada cewa El-Rufa’i ya samu nasara ne a siyasa ciki har da mukamin minista da ya rike sakamakon jam’iyyar PDP ne. A cewarsa, duk abin da ya mallaka a yanzu, ya samu ne ta sanadiyyar jam’iyyar PDP ne.
Lamido ya ce ya samu damar barin PDP ciki har da lokacin da jam’iyya suka yi hadaka wajen haifar APC a 2014, amma ya zabi ya ci gaba da zama a PDP. Ya ce wadanda suka bar jam’iyyar a baya sun yi haka ne saboda fushi, inda suka dunga aibata PDP, to amma yanzu me jam’iyyar APC ta yi musu?
Haka kuma, Lamido ya nanata cewa bai kamata a nemi shugabanci wajen bacin rai na kashin kai ba, shugabanci yana bukatar hakuri, juriya, yi wa al’umma hidima da kuma kasa gaba daya. Ya ce neman shugabanci ta hanyar fusata yana kasancewa ne ta kashin kai ba ta al’ummar kasa ba.
Ya yi gargadin cewa ka da a yi adawa da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta hanyar bukata ta kashin kai ko yin ramako. Ya ce idan manufar ita ce kawar da Tinubu kan karagar mulki, fushi ba shi ne hanya ba. Ya ce ya san yadda zai fuskanci adawa ta fusata.
Lamido ya yi kira a samar da shugabanci mai cike da adalci da kuma martaba hakkokin al’umma. Ya ce ya kamata a mayar da hankali wajen samar da shugabanci mai cike da adalci a Nijeriya maimakon nuna fushin siyasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp