Bayan fashewar da ta girgiza bututun Trans Niger a Bodo dake ƙaramar hukumar Gokana, wata fashewar ta sake auku a wurin ajiyar man fetur na Soku da ke ƙaramar hukumar Akuku Toru a Jihar Ribas.
Ƙungiyar kare muhalli ta YEAC-Nigeria ta tabbatar da afkuwar hakan a wata sanarwa da Daraktanta, Dr. Fyneface Dumnamene Fyneface, ya fitar, inda ya bayyana cewa wasu matasan sa-kai ne suka fara bayar da rahoton fashewar da ta auku da safiyar Lahadi.
- Tinubu Ya Yaba Wa Majalisar Dokoki Kan Amincewa Da Dokar Ta-Ɓaci A Jihar Ribas
- Ba Na Goyon Bayan Dakatar Da Gwamnan Jihar Ribas – Ndume
Sanarwar ta ce an ga walkiya mai ƙarfi da harshen wuta a sararin sama, kuma gobarar na ci gaba da tashi har zuwa lokacin rahoton. Wurin da ta tashi na ƙarƙashin kamfanin iskar Gas na ƙasa (NLNG), kuma rahotanni sun nuna cewa yana da wahalar shiga. Har yanzu ba a tabbatar da musabbabin fashewar ba, amma ana zargin matsalar kayan aiki, ko ƴan ta’adda ko kuma harin da aka kitsa.
Wannan shi ne karo na uku da ake fuskantar irin wannan fashewa a cibiyoyin man fetur a jihar cikin mako guda. Fashewar farko ta auku a Ogoni, sannan na biyu a Oga/Egbema/Ndoni LGA, wanda Shugaba Bola Tinubu ya ambata a jawabin ƙasa na 18 ga Maris, inda ya ayyana dokar ta-ɓaci tare da dakatar da Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, mataimakinsa da Majalisar Dokoki.
Ƙungiyar YEAC ta buƙaci hukumar NOSDRA da ta gudanar da bincike na gaggawa domin gano ainihin dalilin fashewar, tare da tabbatar da cewa waɗanda ke da hannu a lamarin sun fuskanci hukunci bisa tanadin dokar harkokin Man Fetur ta 2021 (PIA).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp