Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan sallah ƙarama.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
- Kamfanonin Sin Za Su Samar Da Hidimomin Kyautata Amfani Da Makamashi Mai Tsafta A Afirka Ta Kudu
- Kantoman Ribas Ya Dakatar Da Dukkanin Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa
Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin Ramadan tare da buƙatar su ci gaba da zaman lafiya, karamci da kyautatawa.
Ya bukaci ‘yan Nijeriya su yi addu’a don samun zaman lafiya da ci gaban ƙasa yayin da suke gudanar da bukukuwan sallah.
Ministan ya aike da wa Musulmi fatan alheri, yana mai fatan wannan lokaci zai kawo farin ciki da haɗin kai ga kowa.