A ko da yaushe shugaban kasar Sin Xi Jinping yana mai da hankali matuka kan aikin kare manyan koguna biyu wato Rawayen kogi da kogin Yangtse, wadanda al’ummar Sinawa suka dauke su a matsayin mahaifiyarsu, musamman ma a cikin shekaru goma da suka gabata.
A cikin wadannan shekaru goma, kasar Sin ta yi iyakacin kokarin kyautata muhallin halittu masu rai da marasa rai a kewayen Rawayen kogi, domin rage zaizayar kasa, kuma ta samu sakamako mai gamsarwa, har matsakaicin yawan lakan da aka zuba cikin Rawayen kogi ya ragu da tan miliyan 300 zuwa 500 a kowace shekara, kuma fadin yankunan zaizayar kasa dake kewayen Rawayen kogin da aka gyara a cikin shekaru goma da suka gabata ya kai muraba’in kilomita dubu 26 da dari 8.
Haka kuma kasar Sin tana himmantuwa kan aikin rage gurbataccen ruwan kogin Yangtse, ta yadda za a cimma burin tabbatar da ingancin ruwan kogin.
Kawo yanzu ruwa mai inganci na kogin Yangtse ya riga ya kai sama da kaso 97 bisa dari, yankunan dake bakin kogin sun kasance ni’imtattun wuraren shakatawa ga mazauna biranen kasar. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)