Kimanin kaso 6 na mutane a fadin duniya ne suka yi ammana cewa, nan gaba, duniya za ta kasance karkashin iko kasa daya tilo wato ko Amurka ko kasar Sin, yayin da kaso 34, rukuni mafi yawa, suke ganin cewa, abu mafi yuwuwa shi ne, samun kasa fiye da daya mai karfin fada aji a duniya fiye.
Wannan sakamakon nazari ne da cibiyar bincike ta CGTN da cibiyar tattara ra’ayoyin jama’a ta jami’ar Renmin ta kasar Sin suka gudanar, wanda ya nazarci mutane daga kasashe 22, ciki har da Amurka da New Zealand da Japan da Indiya da Masar da Nijeriya. (Fa’iza Mustapha)