Wani iftila’i ya afku a ranar Sallah a Jihar Gombe inda mutane biyu suka rasu sakamakon yamutsin da ya ɓarke a tsakiyar filin sallar idi. Abin ya faru ne da karfe 10:45 na safe bayan an gama Sallar Eid da Limamin Gombe ya jagoranta, kuma gwamnan jihar Inuwa Yahaya da Sarkin Gombe Abubakar Shehu Abubakar suka halarta.
Daga binciken LEADERSHIP, tarzomar ta faru ne a bakin kofar fitowa lokacin da jama’a da yawa suka yi gaggawar ficewa. An bayyana cewa aƙalla mutane 22 ne yamutsin ya shafa, ciki har da mutanen biyu da suka mutu.
- Gobe Ta Ke Sallah A Nijeriya – Sarkin Musulmi
- Bayan Hukuncin ‘Yansanda, Sarki Sanusi II Ya Soke Hawan Sallah
Kakakin Ƴansandan jihar Gombe, Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa tarzomar ta faru ne sakamakon gaggawar da mata da yara suka yi na yunƙurin ficewa, tare da zafi mai tsanani. “Motar agajin gaggawa ta Gwamnatin Jihar Gombe sun ɗauki marasa lafiya 15 zuwa Asibitin Zainab Bulkachuwa, yayin da aka kwashe wasu bakwai zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya.
Sai dai kuma, likitoci sun tabbatar da mutuwar ‘yan mata biyu – Aisha Salisu Ahmed ‘yar shekara hudu da rabi, da Maryam Abdullahi Gwani ‘yar shekara huɗu,” in ji shi.
‘Yansandan sun ba da shawarar buɗe duk kofofin shiga da fita domin sauƙaƙe zirga-zirgar masu ibada, musamman bayan Sallah. Sun kuma danganta yamutsin da ƙarancin hanyoyin fitowa daidai gwargwado bayan an gama Sallah.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp