Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ta janye dakatarwar da ta yi wa kocinta, Usman Abdallah, bayan shafe watanni.
An dakatar da Abdallah ne a watan Fabrairu, sakamakon rashin samun nasara a wasannin da suka gabata, tare da wasu kalaman da ƙungiyar ta ce bai dace ya furta ba ga magoya bayanta.
- Abba Ya Nemi Gwamnatin Edo Ta Biya Diyyar Matafiyan Da Aka Kashe A Uromi
- Sanata Yari Zai Tallafa Wa Marayu 20,000 A Zamfara
Wannan ya faru ne bayan wasan da Pillars ta tashi kunnen doki da Bayelsa United a filin wasa na Sani Abacha ranar 22 ga watan Fabrairu.
Tun daga lokacin, mataimakin kocin kungiyar, Ahmed Garba Yaro-Yaro, ke riÆ™e ragamar horar da ‘yan wasan, har ma aka Æ™ara tsawaita dakatarwar a farkon watan Maris.
A yanzu dai an warware matsalar, kuma Usman Abdallah ya koma bakin aikinsa.
Ƙungiyar ta Kano Pillars ta tabbatar da hakan a shafinta na X da rubutun “Barka Da Dawowa Koci”.
A halin yanzu, Kano Pillars na matsayi na takwas a teburin NPFL, da maki 44 bayan buga wasanni 31.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp