Wani kwararre a Kungiyar Bunkasa Aikin Noma A Nahiyar Afirka (AUDA-NEPAD), Farfesa Olalekan Akinbo, ya yi kira da a rungumi aikin noma da kayan fasahar zamani, musamman domin kara samar da wadataccen abinci da kuma kara bunkasa fannin a Nijeriya.
Akinbo, wanda ya yi wannan kira a hirarsa da kafar dillancin labarai ta kasa a Abuja, ya yi nuni da yin hakan na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa fannin.
- 2027: Tsananin Yunwa Zai Hana ‘Yan Nijeriya Sake Zaɓen Jam’iyyar APC – PDP
- CAN: Ƴan Nijeriya Na Cikin Yunwa Da Rashin Tsaro A Mulkin Tinubu
Kazalika ya ce, hakan zai kuma kara yawan amfanin manoma da samar da wadataccen abinci, inda ya sanar da cewa; yana da kyau su ma manoma a karkara su rungumi wannan fasaha domin, havaka nomansu.
“Allah ya albarkaci Nijeriya da kasar noma mai inganci, saboda haka; yin amfani da fasahar zamani ita ce, hanyar da za a magance manyan kalubalen da fannin ke fuskanta, kamar na rashin samun amfani mai yawa, yin asara bayan an yi girbi da sauransu.”.
Kazalika ya ce, duba da karauwar yawan al’ummar wannan kasa tare da bukatar da ake da ita ta abinci da tabbatar da samar da abinci mai yawa, na da matukar muhimmanci a yi amfani da fasahar ta zamani, don magance kalubalen.
A cewar Akinbo, ci gaba da yin dabarun noma na zamani, zai taikama wajen bai wa muhalli da kare kasar da kuma magance kare dumamar yanayi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp