Jami’an ‘yansanda a gundumar Maitama da ke Abuja sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati, inda suka yi kira ga gwamnatin da ta dauki matakan gaggawa kan tabarbarewar tattalin arziki da kuma zargin ‘yansanda na cin zarafin al’umma a kan ikirarin dokar hana aikata laifuka ta yanar gizo.
Zanga-zangar da kungiyar ‘Take-it- Back Movement’ da kungiyoyin fararen hula suka shirya a fadin kasar ya zo daidai da ranar bikin ranar ‘yansanda ta kasa a dandalin Eagle Square da ke Abuja.
- Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas
- Ya Kamata A Yi Adawa Da Kama Karya A Tabbatar Da Adalci
LEADERSHIP ta tuna cewa, hukumomin ‘yansanda sun yi gargadi kan yunkurin duk wata zanga-zanga a fadin Jihohin kasar musamman ma babban birnin tarayya (FCT).
Rundunar ta jaddada cewa, ranar 7 ga watan Afrilu, rana ce da gwamnatin tarayya ta ware a matsayin ranar ‘yansanda ta kasa domin murnar jajircewa da kwazon jami’ai na rundunar ‘yansandan Nijeriya.
Sun yi nuni da cewa, ayyana wannan rana a matsayin ranar gudanar da zanga-zangar, akwai wata makarkashiya a ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp