Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar mai Karamar Hukumar Birni a Jihar Kano, Shaaban Ibrahim Sharada, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADP.
Bayan sauya shekar, take dan majalisar ya karbi tikitin takarar gwamna na jam’iyyar.
- Sauyin Rawayen Kogi Da Kogin Yangtse Cikin Shekaru 10
- Makarantar ‘Aram Mamu Academy’ Ta Yi Bikin Yaye Dalibai Karo Na Uku
An ruwaito cewar wata majiya da INEC a Kano, ta ce Sharada zai yi wa jam’iyyar ADP takara tare da abokin takararsa, Rabiu Bako.
Sharada wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin tsaro da leken asiri, ya shiga neman takarar tikitin kujerar gwamna a jam’iyyar APC amma mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Gawuna ya kayar da shi.
Sai dai bayan faduwa a zaben fidda-gwanin, Sharada, ya kalubalanci zaben inda ya ce ba a yi sahihin zaben fidda-gwani a jihar ba.
A baya-baya an alakanta da shi da komawa jam’iyyar NNPP mai kayan marmari, amma ya musanta wannan labari.