A karo na uku, Makarantar ‘ARAM MAMU ACADEMY’ ta yi bikin yaye wasu daga cikin dalibanta da suka kammala aji na biyar na fannin Nursury a karkashin jagorancin darakta kuma wanda ya kafa makarantar, Muhammad Mamu Zannan Tungar Maje.
An gudanar da bikin ne a harabar makarantar da ke bayan barikin soji ta Zuba a yankin Karamar Hukumar Tafa ta Jihar Neja.
- “Korar Fulani A Edo: Ina Ake So Wadanda Aka Haifa A Jihar Shekara 50 Su Koma?”
- Shugaba Xi Ya Yi Kira Ga Sassan Kasa Da Kasa Da Su Yi Hadin Gwiwar Samar Da Ci Gaban Duniya
Bikin ya samu halartar iyayen yara, malamai da sauran manyan baki daga sassan kasar nan.
Da yake gabatar da jawabi a yayin bikin, Dagacin Tungan Maje Salihu Isyaku, wanda shi ne uban taro, ya sanya wa makarantar albarka, inda ya ce babu abin da za a ce da wanda ya kafa wannan makaranta sai sam barka, sannan kuma ya yi addu’ar Allah ya sa shi Zannan Tungar Maje ya gida jami’a nan gaba.
“Mu dai shekarunmu sun tafi, amma dai ga fadawanmu masu tasowa, don haka ina addu’ar Allah ya sanya albarka, sannan ina gargadin jama’a mu yi zaman lafiya da juna.
Domin shi wanda ya gina wannan makaranta, zama lafiyar da muka yi shi ne ya sa har na ga ya dace na ba shi sarautar Zannan Tungar Maje, domin da ba a yi zaman lafiya da shi ba ka ga da hakan ba ta samu ba, muna girmama shi muna kuma mutunta shi.
Don haka muna fatan jama’a za su zauna lafiya da juna, domin zaman lafiya ya fi komai muhimmanci,”in ji shi.
A karshe ya yi kira ga jama’a su zama masu aikata alheri domin shi ne zai taimaki mutum duniya da lahira.
Da yake bayani kan muhimmacin ilimin mata, Dakta Mamu Alhaji Muhammad, cewa ya yi “Ilimin mata dai yana da muhimmaci ko a addini, saboda a halin yanzu tarbiyyar yara ta koma hannun iyaye mata, to idan kuwa haka ne ya zama ba a tarbiyyantar da su, to za a samu nakasu a tarbiyyar da ake yi musu.
Kuma duk da cewa ana fama da matsalar tsaro bai kamata kuma ya zama dalili na kasa ilmantar da yara mata ba, saboda su ne iyayen gobe.”
A gefe guda kuma ya yi kira ga iyaye masu dora wa ‘ya’yansu talla da su nisanci yin hakan, lallai kuma su kula sosai wajen ba su kariya yadda ya kamata, sannan a tabbatar an kai su makaranta sun koyi ilimin addini da na zamani baki daya, don wannan shi ne zai taimake su wajen zaman rayuwarsu.
Shi ma Abdurrahman Abdullahi, daya daga cikin manyan baki wanda kuma amini ne ga Muhammad Mamu, cewa ya yi wannan shi ne karo na uku da ake yin gabatar da wannan biki na yaye dalibai kuma duk yana halarta.
“Wannan shi ne karo na uku da nake halartar wannan taro na yaye daliban wannan makaranta, saboda amincin da ke tsakannmu da shi, kuma da yake abu ne da ya shafi ilimi abu ne mai muhimmancin gaske, musamman ga al’ummar da suke wannan wuri, kuma zamansa a nan ya kawo alheri da albarka ganin yadda mutane suka halarci wanna wuri ya nuna irin zaman lafiya da yake yi da jama’a, kuma zuwan sarki ma kadai ya isa a fahimci cewa shi mutumin kirki ne tun da gashi ya zo ya zauna har lokacin da ake kammala wannan taro,” in ji shi.
Ya ci gaba cewa ya kamata mu kula da ilimi, domin idan ka kammala karatu ba lallai ne a ce ka samu aikin gwamnati ba, amma ilimi zai saita ka ta yadda za ka iya zama nagartacce.
Ya ce akwai bukatar iyaye su sanya ido su ga mene ne ke zuwa ya komo, hakan kuwa yana da alaka da jituwarsu da malamai, su rika jan su a jiki suna sanin halin da karatunsu ‘ya’yansu ke ciki.
Tun farko, Daraktan makarantar, wanda kuma shi ne ya assasa ta, Muhammad Mamu, Zannan Tungar Maje, cewa ya yi wannan shi ne yaye dalibai na farko daga nazirin farko zuwa firamare, amma daga firamare ta daya zuwa wannan shi ne karo na uku jimilla.
“Kuma wannan makaranta tana da dalibai kusan 200, ni kadai ke daukar nauyin makarantar sai kuma yayyena da suke tallafa min. Ina kira ga gwamnati ta shigo cikin al’amarin makarantu masu zaman kansu, domin makarantu masu zaman kansu na taimaka wa gwamnati kwarai wajen sama wa mutane aikin yi da kuma hanyar rage yawan dalibai.
“To idan aka samu marantu da suke da hazaka wajen koyarwa da tarbiyyantar da yara, ya kamata gwamnati ta shigo ta tallafa wajen gudanar da ayyukansu,” in ji shi.
Ya yi kira ga gwamnati da dage wajen tabbatar da tsaron al’umma da dukiyoyinsu.
Ita ma malama a makarantar kuma uwargida ga Muhammad Mamu, ta nuna farin cikinta bisa ga yadda yara suka nuna bajinta wajen bayyana abubuwan da aka koya musu.
Ta bayyana matakin karbar yara daga gidanjen iyayensu zuwa makaranta da kuma bayan an tashi, inda ta ce, iyaye suna sanya hannu yayin da aka je dauko ‘ya’yansu a motar makarantar da kuma bayan an hannanta su ga iyayensu a ko da yaushe, domin tabbatar da tsaro da lafiyarsu.
An gabatar da dalibai ‘yan shekaru 10 zuwa 13, wadanda suka nuna bajinta wajen gabatar da shirye-shirye a harshen Turanci, kafin daga baya aka gabatar da shiri na al’adun gargajiya na kabilu daban-daban domin kayatar da manyan baki.