Masharhanta da dama na ganin Amurka ta bullo da batun karin harajin fito kan hajojin dake shiga kasar daga sauran kasashe ne domin matsawa abokan huldarta lamba, ta yadda ala tilas za su rusuna a gabanta domin neman sulhu, da mika mata hakkokinsu na cinikayya, ta yadda za ta kwashi riba yayin da sauran sassan kuma za su kwashi hasara.
Kasar Sin na kan gaba cikin kasashen da Amurka ta dorawa karin harajin fito mafi yawa a wannan karo, kuma burin Amurka a nan shi ne kasar Sin ta yi watsi da martanin da ta fara dauka kan matsin lambar Amurka, ko kuma ta fuskanci wani sabon zagayen na kare-karen haraji ba tare da wata hujja ba.
- Sin Ta Kara Wasu Kamfanonin Amurka 12 Cikin Jerin Wadanda Ta Dakatar Da Fitar Musu Da Wasu Kayayyaki Daga Kasar Sin
- Daga Yau Sin Ta Fara Karbar Karin Haraji Na 84% Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Kasar Daga Amurka
To sai dai kuma sabanin tunanin gwamnatin Amurka, kasar Sin ta nace kan matsayinta na turjiya, da kin amincewa da wa’adin Amurka na matsin lamba, ta kuma sha alwashin tunkarar wannan yaki na cinikayya har zuwa karshensa.
Wani muhimmin abun lura ma shi ne ita kanta Amurka ba za ta tsira daga mummunan tasirin wannan yaki na cinikayya da take rura wutarsa ba. Ko shakka babu matakin zai haifarwa Amurka matukar koma bayan tattalin arziki, da hauhawar farashi a cikin gida, da dakile guraben ayyukan yi da sauransu. Tuni ma kasuwannin Amurkan suka fara dandana kudarsu, inda aka fara ganin koma bayan kasuwannin hannayen jari, da gurguncewar sana’o’i sakamakon rashin tabbas da kasar ke fuskanta, yayin da kasar ke tunkarar matsanancin yanayi na komadar tattalin arziki.
Wata manuniya da ka iya haskaka abun da ka iya wakana ga Amurka a wannan karo ita ce irin yadda Amurka ta sha fama da kalubalen hauhawar farashi, da koma baya ga sana’ar noma, da ta sarrafa hajoji, yayin da gwamnatin shugaba Trump ta farko ta dauki makamancin wannan mataki a baya. Don haka abu ne a fili, cewa gwamnatin Trump ta yanzu ma za ta dandana kudarta, bisa wannan mataki na karin haraji marar ma’ana da ta sake bullo da shi.
Tuni dai masana, da masu fashin baki suka bayyana illar wannan mataki na Amurka, suna masu cewa kasancewar tattalin arzikin duniya yana sarke da juna, rungumar kariyar cinikayya alama ce ta rashin hangen nesa da toshewar basira. Kuma tuni al’ummun kasa da kasa suka gano makircin da Amurka ta boye karkashin wannan manufa ta karin haraji, don haka dai ba abun da ya ragewa gwamnatin Amurka illa ta lashe amanta, ta gyara babban kuskuren da ta tafka, domin kaucewa yin mummunan da-na-sani.(Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp