Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin ba ta fatan tsunduma cikin yakin cinikayya da na kare-karen haraji, amma kuma ko kadan ba za ta yi gezau ba idan yakin ya tabbata.
Lin Jian, wanda ya bayyana hakan yau Alhamis, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya yi tsokacin ne yayin da yake amsa tambayar da aka yi, dangane da harajin fito da Amurka ta ayyana dorawa na kaso 125 bisa dari, kan hajojin da ake shigarwa kasar daga Sin.
Ya ce, matakin Amurka na mayar da karin haraji wani makami na matsin lamba, da yunkurin cimma moriyar son kai, ya yi matukar illata halastattun iko da moriyar daukacin kasashen duniya.
Daga nan sai ya ce, kasar Sin na aiwatar da matakan ramuwar gayya na wajibi game da cin zalin Amurka, ba kawai don kare ikon mulkin kanta, da kare tsaro da muradun ci gabanta ba ne, har ma da tabbatar da gaskiya da adalci tsakanin sassan kasa da kasa, da wanzar da tsarin cinikayyar sassa daban daban na duniya, da kuma moriyar bai daya ta dukkanin al’ummun duniya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp