A ƙalla shaguna 12 sun ƙone ƙurmus sakamakon gobarar da ta tashi da daddare a Agodi Gate, birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Lamarin ya faru ne a daren Alhamis a ginin Block A na kasuwar Siminti ta Mayegun, Araromi, kamar yadda hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo ta tabbatar.
Shugaban hukumar, Akinyemi Akinyinka, ya bayyana cewa jami’ansu sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:02 na dare, inda nan take suka tura tawaga ƙarƙashin jagorancin Cfs Jimoh. Bayan isarsu, sun tarar da shaguna da dama na ci da wuta, amma cikin gaggawa suka dakile yaɗuwar gobarar zuwa sauran shagunan da ke kusa.
- Gobara Ta Kashe Yaro A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Maiduguri
- Gobara Ta Ƙone Sabon Ginin Ɗakunan Kwanan Ɗalibai Mata Na Jami’ar Sokoto
Akinyinka ya bayyana cewa gobarar ta samo asali ne daga wutar lantarki mai ƙarfi. Ya ƙara da cewa an kare dukiyoyi da darajarsu ta kai biliyoyin Naira a kasuwar, duk da cewa shaguna 12 sun ƙone baki ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp