Ministan ma’aikatar cinikayya na kasar Sin Wang Wentao, ya yi tir da matakin Amurka na kare-karen harajin fito kan hajojin da ake shigarwa kasar, matakin da ya bayyana a matsayin barazana ga daidaitaccen yanayin gudanar cinikayyar duniya, wanda kuma zai gurgunta tsarin bunkasar tattalin arzikin duniya.
Wang, wanda ya bayyana hakan a jiya Juma’a yayin wata tattaunawa ta kafar bidiyo da babbar daraktar kungiyar cinikayya ta duniya WTO Ngozi Okonjo-Iweala, ya kira harajin ramuwar gayya na Amurka da kyakkyawan misali na cin zali daga bangare guda, wanda kuma ya yi gargadin zai fi illata moriyar kasashe masu tasowa, musamman masu karancin ci gaba, zai kuma iya kaiwa ga jefa jama’a cikin mawuyacin halin jin kai.
Wang ya kuma jaddada cewa, karin harajin na Amurka ya sabawa ka’idojin tushe na WTO, ya gurgunta tsarin cinikayyar kasa da kasa, tare da lalata tushen gudanar da cudanyar cinikayya ta duniya. La’akari da hakan, kasar Sin ta dauki kwararan matakai don kare halastattun hakkokinta, kuma za ta kare gaskiya da adalci a tsakanin sassan kasa da kasa.
A nata martani kuwa, Okonjo-Iweala ta ce, karuwar takun saka ta fuskar cinikayya ya haifar da babban kalubale ga tsarin bunkasar cinikayya da tattalin arzikin duniya. Don haka ta jaddada muhimmancin rungumar budadden salo na bin ka’idar cudanyar mabambantan sassa, kana ta jaddada wajibcin warware dukkanin takaddama ta hanyar tattaunawa mai ma’ana karkashin dandalin WTO. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp