Aƙalla mutum 45 sun kwanta dama a daren Lahadi, a Zike da Kimakpa, da ke Kwall, na ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato, bayan wani hari.
Wannan harin ya faru ne kwanaki kaɗan da aka samu makamancinsa a ƙaramar hukumar Bokkos, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 52 da kuma asarar dukiya da dama da ta kai miliyoyin naira.
- Yawan Jigilar Kayayyakin Da Aka Yi Ta Layin Dogo Na Sin Ya Karu A Rubu’in Farko
- Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Dakatar Da Matakin Kare-Karen Harajin Fito Kan Hajojin Da Ake Shigarwa Kasar
Sakataren Ƙungiyar Ci gaban Irigwe, Danjuma Dickson Auta, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a Jos, inda ya ce harin ya faru misalin ƙarfe 8:00 na dare ranar Lahadi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 47 tare da barin wasu da dama da raunuka.
Sai dai har yanzu rundunar ‘yansandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa ba kan lamarin, kuma ƙoƙarin da samun martaninsu ya ci tura.
A gefe guda kuma, gwamnatin jihar Filato ta nuna damuwa kan hare-haren da ake samu a wasu sassan faɗin jihar, lamarin da ke ƙara haifar da damuwa a zuƙatan jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp