Jaridar kasuwanci mafi girma a fadin Nijeriya, NATIONAL ECONOMY Newspaper, za ta koma fita mako-mako daga ranar 29 ga watan Agustan 2022.
Jaridar National Economy dai tana karkashin kamfanin buga jaridar LEADERSHIP ne wacce take fita kowace rana tun daga ranar Alhamis na watan Fabrairun 2020 wacce ta maida hankali wajen gudanar da aikin jarida kan harkokin kasuwanci a Nijeriya da gudanar da binciken kwakwaf tare da yin rahotonni kan harkokin kasuwanci da tattalin arziki a cikin shekaru biyu da wata bakwai da ta shafe tana fita kowace rana.
- Kaso 6 Na Al’umma Ne Kadai Ke Ganin Duniya Za Ta Kasance Karkashin Ikon Amurka
- Matar Shugaban Kasar Amurka Ta Kamu Da COVID-19
Jaridar ya bada gudunmawa sosai wajen kyautata harkokin kasuwanci da tattalin arziki ta hanyar nakaltowa daga masana da fasihai domin su yi sharhi kan lamuran da suka shafi kasuwanci da tattalin arziki da ankarar da wadanda suka dace a fannin da ke bukatar gyaran fuska.
Kamar yadda shugaban sashin labaru na jaridar NATIONAL ECONOMY, Mista Bayo Amodu ke cewa, sauyin an yi ne da zimmar ingantawa da kyautata jaridar tare da bunkasa aiki domin masu karanta jaridar da abokan huldar kasuwancinta su kara gamsuwa, ya kuma ce ba za su rage ingancin abubuwan da suke wallafa a jaridar ba illa ma su kara.
Ya ce, jaridar ta na da shafin yanar gizo mafi inganci ta addireshi www.nationaleconomy.com da suke wallafa labaran da suka shafi harkokin kasuwanci a kowani lokaci a kowace rana.
Ya ce, “A bisa manufar jaridar tattalin arziki ta National Economy ta kasancewa jaridar wacce ke maida hankali wajen wallafa labarai da mukaloli da batutuwan da suka shafi harkokin kasuwanci da tattalin arziki ga jama’a da kuma kamfanoni, bisa gaskiya da kwarewa hadi da sahihan batutuwa, muna tabbatar wa masu karatu da hulda da mu cewa za mu ci gaba da kara himma wajen hidimta musu.
‘‘Kamar yadda kuka sani, mun karbu sosai mun kuma shahara sosai wajen samar da labaran da suka shafi harkokin kasuwanci da tattalin arziki don mun kai kwaloluwar mataki a fagen yada labaran kasuwanci a Nijeriya.
“Ta hanyar fasahar sadarwar zamani, jaridarmu da muke fitarwa muke kuma yadawa hatta ta hanyar E-paper dubun-dubatan jama’a a cikin lunguna da sakona da kasar nan da kasashen waje ke karanta jaridar duk rana.
‘‘Shafinmu ta yanar gizo, nationaleconomy.com shi ma na samun dubban maziyarta a kowani lokaci. Mun yi amanar cewa komawa mako-mako da za mu yi, zai ba mu dama mu kara azama da kwazo wajen muka hidima fiye da yadda yanzu, ta hanyar fito da muhimman labaran kasuwanci da tattalin arziki, nazari da sharhi.”
Shugaban labarun ya kuma ce shafin nasu na yanar gizo zai cigaba da wallafa labarai a kowani lokaci.
Bayo ya kara da cewa muhimman shafukan da suke cikin jaridar kama daga na mukaloli, sharhi, noma, muhawara, kimiyya, batutuwan kasuwanci, masana’antu da sauransu dukka suna daga cikin ababen da za su gaba da fitowa.
Daga bisani ya nuna cewa hukumar gudanarwar jaridar ta nuna godiyarta ga abokan jere musamman masu karanta jaridar duk rana da kuma masu bata talluka tsawon shekarun da ta shafe tana fita duk rana, ya nemi karin hadin kansu kan hakan domin jaridar ta ci gaba da ingantawa.