A daren ranar Talata, 16 ga Afrilu, 2025, za a yi gagarumin wasa a filin wasa na Santiago Bernabeu da ke Madrid.
Ƙungiyar Real Madrid za ta karɓi baƙuncin Arsenal a wasan zagaye na biyu na gasar Zakarun Turai, wanda ake ganin zai zama ɗaya daga cikin manyan wasanni a tarihi.
- Ina Da Ƙwarewar Da Zan Iya Zama Shugaban Ƙasar Nijeriya – Makinde
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 7 A Wani Sabon Hari A Benuwe
A wasan farko da aka fafata a Ingila, Arsenal ta doke Real Madrid da ci 3 da nema a filin wasa na Emirates da ke birnin Landan.
Amma duk da wannan sakamako, ‘yan wasan Real Madrid ba su yarda an gama da su ba.
Sun yi shirin rama wannan kashi da aka ba su a Ingila.
Don su wuce zuwa zagaye na gaba, Real Madrid na buƙatar ta zura ƙwallaye huɗu ba tare da ta bari Arsenal ta zura ƙwallo ko ɗaya ba.
Idan kuma suka ci ƙwallo uku, kamar yadda Arsenal ta ci su, za a ƙara lokaci domin a fidda wanda yi nasara.
Fitaccen ɗan wasan Faransa, Kylian Mbappe, wanda bai taɓa lashe gasar Zakarun Turai ba, yana fatan ya lashe kofin karo na farko tare da Real Madrid.
Wannan wasa zai ba shi damar jan ragamar ƙungiyar don yin nasara a gaban dubban magoya bayanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp