ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 7 A Wani Sabon Hari A Benuwe

by Sadiq
2 years ago
Manoma

‘Yan bindiga sun kashe manoma bakwai tare da jikkata wasu da dama a wani sabon hari da suka kai garin Otobi-Akpa da ke ƙaramar hukumar Otukpo a Jihar Benuwe da yammacin ranar Talata.

Harin ya jefa jama’ar garin cikin fargaba, inda da dama suka fara barin gidajensu domin neman mafaka.

  • Za A Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” Na Harshen Malay
  • Gazawar Gwamnati Kan Kiyaye Rayuka Da Dukiyoyi: Gwamnan Filato Ya Nemi Yafiyar Al’ummar Jihar

Wani mazaunin garin mai suna Alechenu ya ce maharan da ake zargin makiyaya ne sun shiga garin da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, lokacin da mafi yawan mutane ke dawowa daga gonaki.

ADVERTISEMENT

Ya ce suna zuwa, sai suka fara harbe-harbe da ƙone gidaje.

Wani ganau, Elaigwu Idoko, wanda ya shiga cikin tawagar tsaro wajen binciken waɗanda suka ɓace, ya tabbatar da cewa an gano gawarwakin mutum bakwai zuwa yanzu.

LABARAI MASU NASABA

Manoman Yobe Sun Yi Farin Ciki Da Inganta Tsaro, Sun Koka Kan Tsadar Taki

Tinubu Ya Yi Alƙawarin Sake Gina Yankunan Filato Da Rikici Ya Shafa

Ya ce suna ci gaba da bincike a cikin dazuka da ke kusa da garin.

Ɗan majalisar dokokin Jihar Benuwe mai wakiltar mazaɓar Otukpo-Akpa, Kennedy Angbo, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 5:30 na yamma kuma jama’a da dama sun tsere daga garin saboda tsoro.

Wani mazaunin Otobi, Edwin Emma, ya ce wannan ne karo na biyu da ake kai musu hari cikin wata guda.

“Matata da ’ya’yana sun tsere a kafa yanzu haka. Muna buƙatar taimako,” in ji shi.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yansandan Jihar Benuwe, Catherine Anene, bai yi nasara ba domin wayarta a kashe ta ke.

MASU ALAKA

IFAD
Manyan Labarai

Manoman Yobe Sun Yi Farin Ciki Da Inganta Tsaro, Sun Koka Kan Tsadar Taki

November 15, 2026
Tinubu Ya Yi Alƙawarin Sake Gina Yankunan Filato Da Rikici Ya Shafa
Manyan Labarai

Tinubu Ya Yi Alƙawarin Sake Gina Yankunan Filato Da Rikici Ya Shafa

November 14, 2026
Kotu Ta Hana Miji Magana Da Matarsa Tsawon Mako Biyu
Manyan Labarai

Matashi Ya Yi Ƙaryar Mutuwa Don Gudun Ka Da A Kama Shi Kan Zargin Satar Babur

November 14, 2026
Next Post
Matashin Da Ya Ƙware Wajen Kashe Mutane Da Ƙwace Ya Miƙa Kansa Ga ‘Yansanda A Kano

Matashin Da Ya Ƙware Wajen Kashe Mutane Da Ƙwace Ya Miƙa Kansa Ga 'Yansanda A Kano

LABARAI MASU NASABA

Atiku: An Dakatar da Limamin Da Ya Jagoranci Sallar Jam’in Da Muka Yi

Atiku: An Dakatar da Limamin Da Ya Jagoranci Sallar Jam’in Da Muka Yi

November 15, 2026
Manyan Abubuwan Da Suka Faru A Kannywood Makon Da Ya Gabata

Manyan Abubuwan Da Suka Faru A Kannywood Makon Da Ya Gabata

November 15, 2026
Jaruma Teema Ta Fasa Ƙwai Kan Zargin Saya Mata Mota Da Dino Melaye Ya Yi

Jaruma Teema Ta Fasa Ƙwai Kan Zargin Saya Mata Mota Da Dino Melaye Ya Yi

November 15, 2026
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Gudanar Da Taron Farko Na Majalisar Cinikayya Karkashin Tsarin Shawarwarin Tattalin Arziki Da Cinikayya

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Gudanar Da Taron Farko Na Majalisar Cinikayya Karkashin Tsarin Shawarwarin Tattalin Arziki Da Cinikayya

November 15, 2026
IFAD

Manoman Yobe Sun Yi Farin Ciki Da Inganta Tsaro, Sun Koka Kan Tsadar Taki

November 15, 2026
Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Yi Jawabi A Yayin Bikin Bude Taro Na 4 Na Majalisar Ba Da Shawara Kan Harkokin Masana’antu Da Kasuwanci Ta APEC

Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Yi Jawabi A Yayin Bikin Bude Taro Na 4 Na Majalisar Ba Da Shawara Kan Harkokin Masana’antu Da Kasuwanci Ta APEC

November 15, 2026
Shin Abaya Tana Ɗaukar Hukuncin Hijabi? 

Shin Abaya Tana Ɗaukar Hukuncin Hijabi? 

November 15, 2026
Manoma

Na Yi Aure Kafin Na Yi Istibra’i, Ina Mafita?

November 15, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: INEC Na Fuskantar Dambarwar Sahihancin Kundin Rajistar Zaɓe

November 15, 2026
Wang Yi Ya Yi Kira Da A Wanzar Da Tattaunawa Tsakanin Sin Da Amurka

Wang Yi Ya Yi Kira Da A Wanzar Da Tattaunawa Tsakanin Sin Da Amurka

November 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.