Babban hafsan sojin kasa na Nijeriya Laftanar Janar Farouk Yahaya ya bayyana cewa rundunar sojin Nijeriya a shirye take domin tunkarar ‘yan ta’adda a kasar nan, ya kuma bukaci sojojin da su cigaba da farmakar ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga ba kakkautawa.
Janar Yahaya ya bayyana haka ne a ranar Talata a wajen taron karawa juna sani da aka shirya wa hafsoshi da sojoji na shiyya ta 8 dake Barikin Giginya a Sokoto, mai taken “Kara wa Mayaka Karfin gwiwar fatattakar ‘yan Ta’adda.”
Yahaya wanda ya samu wakilcin babban kwamandan runduna ta 8 kuma kwamandan rundunar Operation Hadarin Daji, Manjo Janar Uwem Bassey yace, COAS Yahaya ya ce ya kamata hafsoshi da sojoji su yi amfani da sabbin dabaru a yakin da suke da ‘yan ta’adda.
Yayin da ya amince cewa Nijeriya na fuskantar manyan kalubalen tsaro da suka hada da masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga da kuma masu rajin kafa Kasa; ya kuma roke sojojin da su nuna kwarewa da kwazo wajen gudanar da ayyukansu ta hanyar bin ka’idojin aikin soji.
Da yake tabbatar da cewa sojoji sun samu gagarumar nasara a kan yakin su da ‘yan ta’adda, ya sake karfafawa sojojin gwiwa wajen magance kalubalen tsaron da ke addabar al’ummar kasar, domin tilas ne a yi galaba a kan dukkan makiya Nijeriya.