• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Kawo Karshen Mamayar Da Kamaru Ke Yi Wa Yankunan Nijeriya

byLeadership Hausa
6 months ago
Kamaru

A kwanukan baya ne, ‘yan Nijeriya suka shiga cikin fargaba, biyo bayan bayyanar kutsen da wasu gugun ‘yan ta’adda da suka fito daga kasar Kamaru suka yi, a wani jeje da ke a yankin Efiat a karamar hukuma Mbo, ta jihar Akwa Ibom.

Sai dai, a bisa yunkurin daukar matakan gaggawa, Majalisar Dattawa a ranar 18 na watan Maris, ta kafa kwamitin wucin gadi da zai gudanar da bincike kan wannan batun.

  • Manchester Ta Kai Zagayen Semi Final A Europa Bayan Doke Lyon
  • Sin Da Malaysia Za Su Samar Sabbin Shekaru 50 Masu Muhimmanci Na Dangantakar Kasashen Biyu

Majalisar ta kuma bai wa kwatin wa’adin mako biyu, da ya gabatar mata da rahoton binciken da ya gudanar kan wannan lamarin

Kazalika, Majalisar ta kuma bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu, da ya gaggauta daukar matakai, musamman domin a tabbatar da an bai wa sama da Rijiyon Mai da na Iskar Gas 2,560 da ke a yanin.

Kwamtin ya kunshi, mutane kamar su; Sanata Jimoh Ibrahim dan jam’iyyar APC daga Mazabar Ondo ta Kudu wanda shi ne, Shugaban kwamtin.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Akwai kuma Sanata Adeniyi Adegbonire dan jam’iyyar APC daga mazabar Ondo ta tsakiya, Sanata Seriake Dickson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Bayelsa ta Gabas, Sanata Shehu Lawan Kaka, dan jam’iyyar APC, daga mazabar Borno ta tsakiya.

Sauran sun hada da; Sanata Banigo Ipaligo dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Ribas ta Yamma, Sanata Jarigbe Jarigbe dan jami’yyar PDP, daga Koros Riba ta Arewa, Sanata Ekong Sampson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Akwa Ibom ta Kudu, Sanata Sani Bello dan jami’yyarAPC, daga mazabar Neja ta Arewa sai kuma Sanata Aniekan Bassey, dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Akwa Ibom.

Majalisar ta kafa wannan kwamtin ne, biyo bayan kudurin da Sanata Aniekan Bassey na mazabar Arewa da Gabas daga Akwa Ibom, ya gabatar mata wacce ta yi daidai da dokokin 41 da 51.

Bugu da kari, a cikin kudurin da Sanata Bassey ya gabatar wa da Majalisar Dattawan ya yi gargadi da cewa, kutsen na ‘yan ta’addar daga kasar Kamaru, zai iya shafar tattalin arzikin jihar ta Akwa Ibom

Sanatan ya shedawa Majalisar cewa, yankin na Efiat, da ke a karamar hukumar Mbo a Akwa Ibom, na daga cikin yankin da aka bai wa kasar Kamaru a shekarar 1913, biyo bayan yarjejeniyar Anglo-German ko kuma a hukuncin da yarjejeniyar Babban Kotun Koli ta Duniya Duniya ta yanke a watan Okutobar 2002.

A nan, muna jinjiawa Majalisar ta Dattawa bisa kafa wannan kwamtin mai mambi tara, musamman domin kwamitin ya gudanar da bincike, kan wannan batun, na zargin kutsen ‘yan ta’addar na kasar Kamaru,a wannan yankin.

Sai dai, a wannan lokacin, yana da kyau a ci gaba da tsimayin sakamakon binciken da kuma shawarwarin da kwamtitin zai gabatar wa da Majalisar ta Dattawa kan wannan batun, domin sanin mataki na gaba da za a dauka.

Batu na maganar rikicin kasa, akasari, yana da wuyar lamari, wajen warware wa, musamman duba da cewa, Nijeriya da kasar Kamaru, kasashe ne, da suka gaji iyakoin kasa daga turawan mulkin mallaka, wadanda kuma, tun a baya, ba a fayyace yadda suke ba.

Bugu da kari, wannan lamari ne, mai matukar mahimmanci da ya shafi kasar nan.

Kazalika, ya zama waji, ‘yan Nijeriya su hada kansu, domin kare iyakokin kasar ga dukkan wata barazana, da za ta iya shafar kasar.

Sai dai, damuwar da akasarin ‘yan Nijeriya ke ci gaba da nunawa kan batun shi ne, na rashin mayar da hankali a siyasance, domin lalubo da mafita kan lamari irin wannan.

Mu a nan, muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kasance mai sanya ido sosai da kuma daukar kwararan matakai da za su kasance ba su kai ga zubar da kimar Nijeriya a idon duniya ba, wajen kare yiwa tattalin arzikin kasar nan.

Hakazalika, ya zama wajbi, Nijeriya ta tashi tsaye, wajen kare kasar daga dukkan wani na’ui na barazana daga kere domin kare kasar nan.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio
Manyan Labarai

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025
Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa
Manyan Labarai

Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

October 7, 2025
Next Post
Duk Da Matsin Rayuwa: Bankuna Na Ci Gaba Da Cin Kazamar Riba Ta Hanyar Dora Wa Al’umma Haraji

Duk Da Matsin Rayuwa: Bankuna Na Ci Gaba Da Cin Kazamar Riba Ta Hanyar Dora Wa Al’umma Haraji

LABARAI MASU NASABA

An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version