• English
  • Business News
Monday, July 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Minista Ya Sake Jaddada Ƙudirin Sabunta Kayan Aikin Watsa Labarai Na Gwamnati

by Sulaiman
3 months ago
in Labarai
0
Minista Ya Sake Jaddada Ƙudirin Sabunta Kayan Aikin Watsa Labarai Na Gwamnati
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya ta sabuntawa da kuma inganta dukkanin kayan aikin watsa labarai na gwamnati, a wani ɓangare na ƙoƙarin ta na gyara fagen yaɗa labarai a Nijeriya.

Mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim, ya faɗa a cikin takarda ga manema labarai cewa Ministan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, yayin da yake jawabi a Zauren Taron Manema Labarai da Ministoci na Shekarar 2025, karo na shida, wanda aka gudanar a Cibiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa da ke Abuja.

  • Xi: Daukar Matsayar Kashin Kai Da Danniya Ba Za Su Taba Samun Goyon Bayan Al’umma Ba
  • Boko Haram Sun Kashe Sojoji 2 Da Wasu A Wani Sabon Hari A Borno

Ministan, wanda bai daɗe da dawowa daga Babban Taro Da Bita na Ƙungiyar Masu Watsa Labarai ta Ƙasa (NAB) da aka gudanar a birnin Las Vegas na ƙasar Amurka ba, ya ce taron – mai taken “Fasaha, Madosa, Makoma” – ya ƙunshi musayar ra’ayoyi daga ƙwararru a fannin fasaha da watsa labarai daga sassa daban-daban na duniya.

Labarai Masu Nasaba

Ƴan Arewa Za Su Yi Murna Idan Na Zama Shugaban Ƙasa — Peter Obi

AI Zai Maye Gurbin Ayyuka Miliyan 92 A Duniya – Farfesa Pate

Waɗanda suka take wa Ministan sawu a tafiyar su ne jagororin hukumomin yaɗa labarai da wayar da kai da ke ƙarƙashin ma’aikatar sa.

Ya yi zama daban-daban tare da ƙwararru inda suka tattauna kan yadda za a inganta ƙwarewa da kuma kayan aiki na zamani na kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Nijeriya.

Ya ce: “Ina sanar da ku waɗannan abubuwan ne domin jaddada ƙudirin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an samu cigaba mai ɗorewa a fannin watsa labarai a ƙasar nan.

“Wannan ne ma ya sanya muke gudanar da irin wannan taron bita na ministoci, da kuma shirin ƙaddamar da Taron Tattaunawa da Jama’a a sassan ƙasar nan nan gaba kaɗan.”

Minista

Idris ya kuma bayyana halartar da ya yi a Taron Kasuwanci na Nijeriya da aka yi a birnin Paris, ƙasar Faransa, wanda kamfanin Business France ya shirya.

A gefen taron, Idris ya gana da manyan jami’an hukumar UNESCO domin ƙara inganta shirin kafa Cibiyar Ilimin Kafofin Watsa Labarai a birnin Abuja.

A cewar sa, wannan cibiyar za ta taimaka gaya wajen bunƙasa hazaƙar ‘yan jarida da kuma gina sahihin tsarin yaɗa labarai mai inganci a ƙasar nan.

Ya ce: “Cibiyar za ta taka muhimmiyar rawa wurin ƙara ƙarfin gwiwa da ingancin aikin ‘yan jarida a Nijeriya.”

Idris ya ƙara da cewa shirye-shiryen da ake yi kamar wannan taron bita da kuma Taron Tattaunawa da Jama’a da ke tafe, yana daga cikin dabarun gwamnatin don ƙarfafa gaskiya, ƙarfafa tattaunawa tsakanin gwamnati da al’umma, da kuma ƙarfafa amincewa a tsakanin ɓangarorin biyu.

A yayin taron, Ministan Wutar Lantarki, Cif Adebayo Adelabu, ya yi bayani kan matakan da ake ɗauka don gyara ɓangaren wutar lantarki domin tallafa wa shirin gwamnati na bunƙasa masana’antu da tabbatar da isasshiyar wutar lantarki ga ‘yan Nijeriya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Xi: Daukar Matsayar Kashin Kai Da Danniya Ba Za Su Taba Samun Goyon Bayan Al’umma Ba

Next Post

2027: Dalilan Da Suka Sa ‘Yan Siyasa Ke Tururuwar Zuwa Gidan Buhari A Kaduna

Related

Ƴan Arewa Za Su Yi Murna Idan Na Zama Shugaban Ƙasa — Peter Obi
Labarai

Ƴan Arewa Za Su Yi Murna Idan Na Zama Shugaban Ƙasa — Peter Obi

1 hour ago
AI Zai Maye Gurbin Ayyuka Miliyan 92 A Duniya – Farfesa Pate
Ilimi

AI Zai Maye Gurbin Ayyuka Miliyan 92 A Duniya – Farfesa Pate

2 hours ago
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga Tare Da Kwato Makamai A Jihar Filato
Da ɗumi-ɗuminsa

‘Yan Boko Haram Sun Kashe Mutane 9, Tare Da Jikkata Wasu Mutum 4 A Borno

14 hours ago
Sanata Dickson Ya Buƙaci ‘Yan Nijeriya Da Su Yi Yaƙi Da Matsalar Sayen Ƙuri’a
Labarai

Sanata Dickson Ya Buƙaci ‘Yan Nijeriya Da Su Yi Yaƙi Da Matsalar Sayen Ƙuri’a

15 hours ago
Yankin Kudu-Maso-Kudu Zai Cimma Matsaya Ɗaya Kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki – Sanata Dickson
Labarai

Yankin Kudu-Maso-Kudu Zai Cimma Matsaya Ɗaya Kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki – Sanata Dickson

16 hours ago
Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha
Manyan Labarai

Ranar Talata Mai Zuwa Zan Koma Zauren Majalisar Dattawa – Sanata Natasha

19 hours ago
Next Post
2027: Dalilan Da Suka Sa ‘Yan Siyasa Ke Tururuwar Zuwa Gidan Buhari A Kaduna

2027: Dalilan Da Suka Sa ‘Yan Siyasa Ke Tururuwar Zuwa Gidan Buhari A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Ƴan Arewa Za Su Yi Murna Idan Na Zama Shugaban Ƙasa — Peter Obi

Ƴan Arewa Za Su Yi Murna Idan Na Zama Shugaban Ƙasa — Peter Obi

July 7, 2025
AI Zai Maye Gurbin Ayyuka Miliyan 92 A Duniya – Farfesa Pate

AI Zai Maye Gurbin Ayyuka Miliyan 92 A Duniya – Farfesa Pate

July 7, 2025
Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Tunisiya Da Ci 3-0 A Moroko

Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Tunisiya Da Ci 3-0 A Moroko

July 6, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga Tare Da Kwato Makamai A Jihar Filato

‘Yan Boko Haram Sun Kashe Mutane 9, Tare Da Jikkata Wasu Mutum 4 A Borno

July 6, 2025
Mataimakin Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Sabbin Fasahohin Kimiyya A Fannin Aikin Gona Da Kiwon Lafiya

Mataimakin Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Sabbin Fasahohin Kimiyya A Fannin Aikin Gona Da Kiwon Lafiya

July 6, 2025
Sanata Dickson Ya Buƙaci ‘Yan Nijeriya Da Su Yi Yaƙi Da Matsalar Sayen Ƙuri’a

Sanata Dickson Ya Buƙaci ‘Yan Nijeriya Da Su Yi Yaƙi Da Matsalar Sayen Ƙuri’a

July 6, 2025
Xi Ya Ba Da Amsar Wasikar Matasan Amurka ’Yan Wasan Kwallon Pickle Bisa Ziyartar Sin

Xi Ya Ba Da Amsar Wasikar Matasan Amurka ’Yan Wasan Kwallon Pickle Bisa Ziyartar Sin

July 6, 2025
Yankin Kudu-Maso-Kudu Zai Cimma Matsaya Ɗaya Kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki – Sanata Dickson

Yankin Kudu-Maso-Kudu Zai Cimma Matsaya Ɗaya Kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki – Sanata Dickson

July 6, 2025
Sin Za Ta Fadada Hadin Gwiwa Da Brazil A Fannin Tattalin Arzikin Fasahar Zamani Da Sha’anin Jiragen Sama

Sin Za Ta Fadada Hadin Gwiwa Da Brazil A Fannin Tattalin Arzikin Fasahar Zamani Da Sha’anin Jiragen Sama

July 6, 2025
Hadimin Gwamnan Yobe Ya Fice Daga APC Ya Koma Jam’iyyar ADC

Hadimin Gwamnan Yobe Ya Fice Daga APC Ya Koma Jam’iyyar ADC

July 6, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.