Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sake bitar sha’anin kasar Libya da takunkumin da aka kakaba mata a jiya Alhamis 17 ga watan nan, inda wakilin kasar Sin ya yi kira ga kasashen duniya da su kara zuba jari a kasar ta Libya, da kuma kara kaimi ga bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar.
Mataimakin babban wakilin kasar Sin a MDD, Sun Lei, ya bayyana cewa, bisa goyon bayan da ake samu daga kasashen duniya, al’ummar kasar Libya na ci gaba da ingiza maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun wadata a kasar.
Sai dai kuma, a wani sa’in, ya ce, har yanzu Libya na ci gaba da fama da tabarbarewar sha’anin siyasa, kuma ana kara samun matsin lamba a kan ayyukan jin kai da na tattalin arziki. Don haka, ya kamata kasashen duniya da kwamitin sulhu su goyi bayan kasar ta Libya wajen farfado da harkokin siyasa, da yin duk wani kokari na tabbatar da zaman lumana a kasar baki daya, da taimaka wa kasar ta fuskar shawo kan kalubalen tattalin arziki da na jin kai, tare da hada hannu wajen tallafa wa kasar ta fita daga kangin mawuyacin halin da take ciki. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp